An Tafka Asarar Dukiyar Miliyoyin Naira Sakamakon Gobara Da Ta Faru A Jigawa
- Gobara ta yi barna a kauyukan Malamawar Dangoli, Karangi, da Kwalele a karamar hukumar Kiyawa ta Jihar Jigawa inda aka rasa dabobbi, kayan abinci da wasu kayayyaki
- DSP Lawan Shiisu Adam, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Jigawa ya tabbatar da afkuwar gobarar da aka ce ta faru a ranar Lahadi
- Ibrahim Abdullahi El-Y Gumel, shugaban hukumar kashe gobara na jihar Jigawa shima ya tabbatar, ya kuma ce kona kara ne ya janyo gobarar
Kiyawa, Jihar Jigawa - Mummunan gobara ta lalata kayayyaki na miliyoyin naira a kauyukan Malamawar Dangoli, Karangi, da Kwalele a karamar hukumar Kiyawa ta Jihar Jigawa.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gobarar da ya faru a ranar Lahadi 5 ga watan Maris na 2023 ta lalata gidaje, shanu da awaki, dabobi, kayan amfanin gona da wasu abubuwan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tawagar jami'an yan sanda da masu kashe gobara daga jiha, tarayya da filin tashi da saukan jiragen sama sun tafi wurin da abin ya faru don kashe gobarar.
Mai magana da yawun yan sandan jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da afkuwar lamarin yana mai cewa:
"Kawo yanzu ba a rasa rai ko daya ba, amma wasu iyalai da ake zargin sun tsere don ceton ransu ba a gansu ba."
Shugaban hukumar kashe gobara ya bayyana abin da ya janyo wutan
Shugaban hukumar kashe gobara na jihar Jigawa, Ibrahim Abdullahi El-Y Gumel ya ce kona kara da wasu mazauna kauyen da ba a san ko su wanene suka yi ba ya janyo afkuwar lamarin.
Ya yi kira ga mutane su dena kona dazuka da bola a kusa da kauyukan musamman a yanzu lokacin bazara.
Ya ce:
"Muna kira ga mutane su yi takatsantsan da wuta kuma su dena kona dazuka da bola da ke kauyen ko kusa da su."
Ana cigaba da bincike kan sanadin gobarar, hukumomi na shawartar mutane su cigaba da sa ido da kulawa ta musamman don kare afkuwar irin haka a gaba, Channels TV ta rahoto.
An yi gobara a babban kasuwar Maiduguri ta Jihar Borno
A wani labarin kun ji cewa gobara ta tashi a babban kasuwar Maiduguri da ake yi wa lakaci da 'Monday Market'.
Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, gobarar ta tashi ne misalin karfe 2 na daren ranar Lahadi, ta kuma bazau zuwa shaguna daban-daban a cikin kasuwar.
Asali: Legit.ng