Yan Bindiga Sun Halaka Fasto da Ya'yansa Biyu a Jihar Filato

Yan Bindiga Sun Halaka Fasto da Ya'yansa Biyu a Jihar Filato

  • Wasu mahara da ba'a sani ba sun yi ajalin Fasto da 'ya'yansa biyu ranar Lahadi da safe a kauyen Ganawuri da ke jihar Filato
  • Shugaban matasan garin ya bayyana yadda lamarin ya faro tun ranar Laraba, ya ce yana tsammanin harin ɗaukar fansa ne
  • Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sanda, Alfred Alabo, ya ce jami'ai sun fara bincike don gano waɗanda suka kitsa harin

Plateau - 'Yan bindiga sun kashe Rabaran Musa Hyok na Majami'ar Christ in Nation da 'ya'yansa guda biyu a ƙauyen Ganawuri, da ke ƙaramar hukumar Riyom a jihar Filato.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda reshen jihar Filato, Alfred Alabo, ya tabbatar da faruwar lamarin jiya a Jos, babban birnin jihar.

Harin yan bindiga a Filato.
Yan Bindiga Sun Halaka Fasto da Ya'yansa Biyu a Jihar Filato Hoto: vanguardngr
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta rahoto mai magana da yawun 'yan sandan na cewa maharan sun kashe Malamin Cocin ne ranar Lahadi da safe.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Rundunar Yan Sanda Ta Ayyana Neman Ɗan Takarar Gwamna da Wasu 9 Ruwa a Jallo

"Tuni rundunar 'yan sanda ta buɗe babin bincike domin bankado duk masu hannu da aikata wannan ɗanyen aikin," inji Alabo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda rikicin ya faro

Shugaban matasan kauyen, Mista Song Moro, ya yi zargin cewa harin na ɗaukar fansa ne biyo bayan kashe wasu matasan Fulani su uku a garin.

A kalamansa ya ce:

"Lamarin ya soma ne daga gardama ya sauya salo zuwa rikici har ta kai ga ya yi sanadin kashe matasan Fulani guda uku duk da kokarin zaman sulhu da rokon a kwantar da hankula."
"Muna zargin cewa wannan batu ne ya haddasa kai hari kan iyalan da ba su ji ba kuma ba su gani ba, waɗanda ba su san komai game da abinda ya auku ba ranar Laraba da ta shige."

Mista Baro ya ce tuni aka binne gawar Malamin da 'ya'yansa cikin ɗar-ɗar da tashin hankali da kuma tsaurara matakan tsaro a yankin Ganawuri, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An Kuma: 'Yan Bindiga Sun Sake Kai Sabon Mummunan Hari a Jihar Kaduna

Ana neman ɗan takarar gwamna ruwa a jallo

A wani labarin kuma Yan Sanda Sun Ayyana Neman Dan Takarar Gwamnan APGA Kan Kisan Basarake

Kakakin yan sandan jihar Ebonyi ya ce hukumar 'yan sanda na neman wasu mutane 10 ruwa a jallo bisa zargin hannu a kitsa kisan wani Basarake.

Rahotanni sun bayyana cewa a makon da ya gabata ranar Litinin, wasu 'yan bindiga suka halaka Basaraken kuma ana zargin ɗan takarar gwamna ya ba da gudummuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262