Sabon Harin Zamfara Da Kano: Bola Tinubu Ya Ce a Taka Birki, Dole a Daina Kashe-Kashe a Najeriya
- Asiwaju Bola Tinubu ya yi Allah wadai da harin da yan bindiga suka kaiwa jami'an tsaro a jihar Zamfara
- Zababben shugaban kasar wanda ya ce kisan rashin hankali bai da gurbi a kasar ya nemi a binciki kisan da aka yi wa maigari a Kano
- Tinubu ya kuma mika ta'aziyya ga Sheikh Gumi da iyalan marigayi Sani Abacha kan rashi da suka yi
Zamfara - Zababben shugaban kasar Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa kashe-kashen rashin hankali bai da hurumi a kasar nan.
Tinubu ya fadi hakan ne yayin da yake martani ne ga mummunan harin da yan bindiga suka kai kan ofishin yan sanda a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara, jaridar The Cable ta rahoto.
A safiyar ranar Lahadi, 5 ga watan Maris ne yan bindiga suka farmaki yankin inda suka kashe shugaban yan sanda na yankin wato DPO, Kazeem Raheem, da wasu jami'an tsaro biyuu.
A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun hadimininsa, Abdulaziz Abdulaziz, a ranar Litinin, Tinubu ya bayyana cewa ya zama dole al'ummar kasar su hada kansu don cin nasara a kan wadannan makasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya ce:
"A matsayinmu na kasa, ya zama dole mu hade don cin galaba kan wadannan makasan yan ta'addan a lokaci daya.
"Bai kamata kisan rashin hankali da zalunci irin wannan ya samu hurumi a kasarmu ba."
Tinubu ya kuma ce ya kamata ayi bincike a kan kisan hakimin Maigari a jihar Kano, wanda shine mahaifin Munir Dahiru Maigari, shugaban karamar hukumar Rimin Gado, rahoton Premium Times.
Tinubu ya mika ta'aziyya ga Sheikh Gumi da iyalan Abacha
Zababben shugaban kasar ya kuma mika ta'aziyya ga iyalan Ahmad Gumi, malamin addinin Musulunci da na Sani Abacha, tsohon shugaban kasar Najeriya.
Yayin da Gumi ya rasa mahaifiyarsa, iyalan Abacha sun rasa dansu mai suna Abdullahi.
"Yana da matukar taba zuciya rabuwa da masoyi, a kowani yanayi kuma duk shekarunsa.
"Ba za mu iya ja da nufin Allah ba amma addu'a kawai za mu iya yi shine rokon Allah madaukakin sarki ya ji kan mamatan."
A wani labari na daban, mun ji cewa kungiyoyin jama'a sun fara kamun kafa don samun mukamai a gwamnatin Bola Tinubu mai kamawa.
Asali: Legit.ng