Yan Bindiga Sun Sake Shiga Kaduna, Sun Yi Awon Gaba da Sama da Mutum 10
- Yan bindiga sun kai farmaki garin Janjala da ke ƙaramar hukumar Kagarko a jihar Kaduna ranar Lahadi
- Mazauna garin sun bayyana cewa maharan sun yi awon gaba da matar aure da yaranta biyu da kuma wasu mutane 9
- Tara daga ciki sun kuɓuta amma har kawo yanzun hukumar 'yan sanda ba ta ce komai ba game da sabon harin
Kaduna - 'Yan bindiga sun kuma sace wata matar aure, biyu daga cikin 'ya'yanta da kuma wasu mutane 9 a kauyen Janjala, karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.
Daily Trust tattaro cewa kauyen Janjala a 'yan watannin da suka shige, suna fama da yawaitar hare-haren 'yan fashin daji, waɗanda ke garkuwa da mazauna kauyen.
Wani mazaunin garin, Dauda Bala, ya yabbatar da aukuwar sabon harin garkuwa ta wayar salula ranar Lahadi. Ya faɗi sunan matar, Hauwa Ummi Abubakar da yaranta biyu, Sadiya da Idris.
Haka nan Madakin Janjala, Samaila Babangida, ya tabbatar da lamarin amma ya ce mutum 9 daga cikin waɗanda aka sace sun gudo daga hannun yan bindigan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Babu wata sanarwa a hukumance daga bakin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda game da sabon harin garkuwa da mutanen har kawo yanzu.
Garuwa da mutanen da basu ji ba kuma ba su gani ba na ɗaya daga cikin matsalolin tsaron da arewacin Najeriya ke fama da su musamman shiyyar arewa maso gabas.
Yan bindigan daji, waɗanda Kotu ta ayyana su 'yan ta'adda na kai farmakin ta'addanci, su kashe fararen hula da jami'an tsaro ko su sace mutane don neman kudin fansa.
Ko a jiya mun kawo muku rahoton yadda wasu yan bindiga suka hallaka DPO na yan sanda, da wasu dakaru a jihar Zamfara, kamar yadda Punch ta ruwaito.
An Harbe Wani Basarake Har Lahira a Jihar Kano
A wani labarin kuma Miyagun yan bindiga sun je har gida, sun kashe Dagaci a yankin karamar hukumar Rimin Gado, Kano
Basarken da aka kashe, mahaifi ne ga shugaban karamar hukumar, Barista Munir Ɗahiru Maigari, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin.
A cewar ciyaman din ba zasu ce komai kan dalilin kashe masu mahaifi ba a halin yanzun, amma ya faɗi yadda lamarin ya faru da daddare.
Asali: Legit.ng