Mai Kula Da Bukatun Fasinjojin Jirgin Sama Ta Yi Ciki, Bidiyo Ya Mamaye Intanet
- Wata zankadediyar mai kula da Fasinjojin jirgi ta haddasa cece kuce yayin da ta bayyana cewa wata 2 da samun juna biyu amna ba ta sani ba
- Da yawan yan uwanta mata da suka maida martani sun tambayeta ko ta ga al'ada a tsawon waɗannan watanni biyun
- Matar tace bayan watanni 5 ta ɗauki hutun kula da juna biyu domin kula da kanta da kuma jaririn da zata haifa
Wata kyakkyawar mata (@husnaaaa_d) mai aiki a matsayin mai kula da fasinjojin jirgin sama ta wallafa bidiyon rayuwar cikinta da kuma abubuwan da ta fuskanta tsawon watanni 9.
Matar ta bayyana cewa ba ta san tana ɗauke da juna biyu ba har sai da ya shafe watanni biyu kuma a tsawon wannan lokacin ba abinda ta fasa na aikinta a cikin jirgi.
Ma'aikaciyar jirgin ta bayyana labarinta
A cewarta, ta gaya wa mijinta abokin rayuwarta cewa suna gab da samun haihuwa a ranar da Likita ya gwada ta. Matar ta ce ta rame sosai a laulayin ciki na farko.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Bugu da ƙari, kyakkyawar matar ta bayyana cewa ta ci gaba da aikinta na baiwa fasinjojin haƙƙinsu tsawon watanni biyar bayan tabbatar da tana ɗauke da juna biyu.
Da yawan mutanen da suka kalli bidiyon sun ce ba su taba ganin mai aikin jirgin sama ɗauke da ciki ba yayin tafiye-tafiyensu.
Kalli bidiyon anan
Zuwa yanzun sama da mutane 500 suka maida mata martani yayin da akalla mutane 200,000 suka kalli bidiyon.
Wasu daga cikin martanin jama'a
@Bahdgirl_april ta tambayeta da cewa:
"Wace makarantar koyon aikin jirgin sama kika halarta nima burina na zama ma'aikaciyar jirgi."
Renisha Kandhai ta ce:
"Ta ya zaki ce baki sani ba? Kin ga jinin Al'adarki yadda kika saba gani a lokacin?"
adventurousness ya ce:
"Karon farko kenan amma ban taɓa ganin mace mai ciki tana aiki a jirgin sama ba."
Angelic ta ce:
"Ta ya mace zata ɗauki ciki ba ta sani ba, ni da zaran al'adata ta makara da kwana biyu shiga damuwa nake, ina taya ki murna."
Ta maida masu da nartanin cewa, "Wasu matan na yin Al'ada lokacin da suke ɗauke da juna biyu."
A wani labarin kuma Wata matar aure ta bayyana matsanancin halin da take ciki da mijinta kan rashin lafiyar mahaifiyarsa
A cewar matashiyar matar, mijinta ya matsa mata lamba dole sai ta bayar da ƙodarta guda an dasawa mahaifiyarsa da ke kwance ba lafiya.
Sai dai ta bayyana cewa ba zata amince da buƙatar sahibin na ta ba bisa wasu dalilai da ta zayyano.
Asali: Legit.ng