Inna lillahi Wa inna Ilaihi Rajiun, Mahaifiyar Sheikh Ahmad Gumi Ta Rasu

Inna lillahi Wa inna Ilaihi Rajiun, Mahaifiyar Sheikh Ahmad Gumi Ta Rasu

  • Inna Lillahi wa inna ialihi raji'un, kowace rai zata ɗanɗani mutuwa, Allah ya yi wa mahaifiyar Sheikh Ahmad Mahmud Gumi rasuwa
  • Fitaccen Malamin ya bayyana cewa ta rasu ne da misalin karfe 5:30 na yamma yau Lahadi 5 ga watan Maris, 2023
  • Za'a mata Jana'iza gobe Litinin da Azahar a kofar gidan marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da ke Unguwan Sarki Kaduna

Kaduna - Mahaifiyar fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan na jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi, ta riga mu gidan gaskiya.

Bayanai sun nuna cewa mahaifiyar Malamin ta rasu ne a wani Asibiti dake birnin tarayya Abuja da yammacin yau Lahadi, 5 ga watan Maris, 2023.

Sheikh Dakta Ahmad Gumi.
Sheikha Dakta Ahmad Abubakar Mahmud Gumi Hoto: Dr. Ahmad Gumi
Asali: UGC

Shehin Malamin ya tabbtar da rasuwar mahaifiyarsa a shafinsa na dandalin sada zumunta Facebook. Ya ce ta rasu da misalin ƙarfe 5:30 na yamma.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Tsohon Dan Majalisar Oyo Ya Mutu Bayan Yar Gajeruwar Rashin Lafiya

Sheikh Gumi ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, da zuciya mai rauni nake sanar da rasuwar mahaifiyata, yau da misalin karfe 5:30 na yamma. Dan Allah ku tama ni roka mata gafara da rahamar Allah."
"Kalamai na karshe da ta faɗa mun mako uku da suka gabata; In Sha Allah, Allah zai sanya ta da 'ya'yanta da jikokinta wuri ɗaya a cikin gidan Aljannah."
"Waɗan nan kalmomi suna kwantar mun da hankali, Allah ya tabbatar da rahamarsa a gareta, Amin."

Za'a mata Janaza Gobe Litinin

Wata sanarwa mai biye wa wannan a shafin Malamin na Facebook ta ce za'a yi Jana'iza gobe Litinin 6 ga watan Maris, 2023 a ƙofar gidan Marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi.

Sanarwan ta ƙara da bayanin cewa za'a gabatar da Jana'iza da Azahar misalin karfe 1:00 a gidansu da ke Anguwar Sarki, GRA bayan Lugard Hall cikin garin Kaduna.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan Bindiga Sun Harbe Basarake Har Lahira a Jihar Kano

A wani labarin kuma Ɗan marigayi shugaban Najeriya a zamanin mulkin Soja, Sani Abacha, ya riga mu gidan gaskiya a Abuja

Abdullahi Abacha, wanda daga shi sai autan tsohon shugaban kasan ya rasu yana da shekaru 36 da haihuwa a duniya.

Bayanai daga iyalan gidan marigayin sun nuna cewa Abdullahi ya rasu ne a cikin barcinsa a gidansa da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel