Wa'adin Tsaffin Naira: Dole Buhari Ya Mutunta Umurnin Kotu, In Ji Shinkafi

Wa'adin Tsaffin Naira: Dole Buhari Ya Mutunta Umurnin Kotu, In Ji Shinkafi

  • Alhaji Sani Abdullahi Shinkafi, jigon jam'iyyar APC a Zamfara ya yaba wa kotun koli kan hukuncin da ta yanke kan wa'adin dena amfani da tsaffin naira
  • Shinkafi ya kuma ce ya zama dole Shugaba Muhammadu Buhari ya mutunta umurnin babban kotun na kasa kasancewarta mafi girma a kasar
  • Jigon na jam'iyyar APC mai mulki a kasa ya jinjinawa gwamnonin jihohin Kaduna, Kogi da Zamfara, ya kuma ce su sake kai Buhari kotu idan bai mutunta umurnin kotu ba

Zamfara - Jigon jam'iyyar APC a jihar Zamfara, Alhaji Sani Abdullahi Shinkafi, ya yaba wa hukuncin kotun koli kan sauya fasalin naira, yana mai kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya mutunta doka, rahoton The Punch.

Da ya ke jawabi ga manema labarai a gidansa da ke Gusau, Shinkafi ya ce dole Buhari ya mutunta hukuncin kotun koli ya bari a cigaba da kashe sabbi da tsaffin nairorin har zuwa ranar 31 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnoni: Buhari Ya Bada Hakuri Kan Canjin Kudi, Ya Bayyana ‘Yan Takaransa

Abdullahi Shinkafi
Jigon APC, Abdullahi Shinkafi, ya ce ya zama dole Buhari ya mutunta umurnin kotun koli. Hoto: PM News Nigeria
Asali: Facebook

Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tunda kotun koli ya yanke hukuncin cewa a cigaba da kashe sabbi da tsaffin naira, babu kowa a kasar duk girmansa da zai saba dokar.
"Ina kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya mutunta umurnin kotu kuma ya umurci CBN ya yi gaggawar sakin kudin ga al'umma."

Shinkafi ya yi bayanin cewa tsarin sabbin nairan ya shafi yan Najeriya da dama wadanda ke rayuwa cikin talauci tun gabatar da dokar.

Emefiele ya bai wa Buhari gurguwar shawara

A cewar Shinkafi, gwmanan CBN Godwin Emefiele ya bawa Buhari gajeruwar shawara, yana mai cewa:

"Ba haka kasashen da suka cigaba suke sauya kudadensu ba."

Ya bada misali da Amurka, Birtaniya da Saudiyya inda aka yi amfani da kudade biyu har lokacin da tsaffin suka kare.

"An canja kudi a kasashe kamar Amurka, Birtaniya, Saudiyya da wasu kasashen da suka cigaba sun canja kudi amma ba su hana amfani da tsaffin kudin cigaban gaggawa ba.

Kara karanta wannan

Gwamna Masari Ya Tattauna Da Buhari Kan Zaben Gwamnan Jihar Katsina

"Abin da suka saba yi shine su bari a cigaba da amfani da tsaffi da sabbin kudin har sai dukkan sabbin sun koma banki."

Shinkafi ya yaba wa Matawalle, El-Rufai da Yahaya Bello

Ya yaba wa gwamnonin jihar Zamfara, Kaduna da Kogi kan gagarumin kokarin da suka yi na ceto kasar daga rushewa baki daya kan sauyin kudin.

Ya shawarci gwamnonin su koma kotu idan Shugaba Buhari, Antoni Janar, AGF, da CBN suka yi yin abin da kotun koli ta umurta.

A wani rahoton kun ji cewa hukumar ICPC ta damke wani Hassan Ahmed da makuden naira da suka hada da tsaffi da sabbi a yayin da mutanen kasa ke fama da karancin kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164