INEC Ta Haramtawa Ma'aikata Masu Sakaci Aiki a Zaben Gwamnoni
- INEC ta ɗauki tsauraran matakai domin magance sake fuskantar kalubale a zaben gwamnoni da ke tafe
- Farfesa Mahmud Yakubu, Ciyaman din hukumar zabe ya haramtawa ma'aikatan da suka yi sakaci sake shiga aikin zabe
- Ya kuma umarci REC na kowace jiha ya gaggauta ɗaukar matakin ladabtarwa kan duk wanda aka kama da wasa yayin aiki
Abuja - Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta haramta wa dukkan ma'aikatan da aka gano sun yi sakaci a zaben shugaban ƙasa da 'yan majalisun tarayya daga shiga aikin zaben gwamnoni mai zuwa.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, ne ya sanar da haka a wurin taronsa da kwamishinonin hukumar (REC) wanda ya gudana a Abuja ranar Asabar, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
"Yayin da muke tunkarar zaben gwamnoni da mambobin majalisar dokokin jihohi ya zama wajibi mu ƙara zage dantse wajen magance kalubalen da muka fuskanta a zaben da ya gabata."
Sakamakon Zabe: Tsoffin Gwamnoni da Ministoci, Sanatoci da Wasu Manya Sun Huro Wa INEC Wuta Kan Abu 1
"Dukkan ma'aikatan da aka gano suna da sakaci, ko waɗanda muka saba aiki da su ne ko masu aikin wucin gadi, ciki harda masu raba kaya da masu tattara sakamako, kada a saka su a zaɓe mai zuwa."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Kowane kwamishinan zabe (INEC) ya gaggauta ɗaukar matakin ladabtarwa kan duk wanda kwararan shaidu suka tabbatar ya tafka kuskure a zaben da ya gabata."
- Farfesa Mahmud Yakubu.
Yakubu ya bayyana cewa wannan taron shi ne karo na uku cikin watanni biyu kuma kamar kowane zama, sun tattauna batutuwan da suka shafi babban zaben 2023.
A cewarsa, sun ƙara nazari kan zaben shugaban kasa da ya wuce mako ɗaya nan baya da kuma zaben gwamnonin da ake tunkara nan da mako ɗaya ranar 11 ga watan Maris.
Shugaban INEC ya yaba da sadaukarwar yan Najeriya da kuma wayewa da fahimtar da jagororin siyasa suka nuna duk da banbanci inuwa a lokacin zaɓe, kamar yadda Punch ta rahoto.
Hadimin gwamnan Ebonyi ya sauya sheka
A wani labarin kuma Hadimin Gwamnan APC Ya Yi Murabus Kwana 7 Gabanin Zaben Gwamnoni
Mai baiwa gwamɓa shawara na musamman kan harkokin matasa da safarar kwayoyi a jihar Ebonyi, Mista Onu, ya yi murabus daga muƙaminsa.
Ya tabbatar da sauya shuke zuwa PDP kana ya ayyana goyon bayansa ga ɗan takarar gwamna, Ifeanyi Chukwuma Odii.
Asali: Legit.ng