Hawaye, Alhini Yayin Da Dan Marigayi Sani Abacha Ya Rasu A Abuja
- Abin bakin ciki ya faru a gidan iyalan Abacha, a yayin da daya cikin babban dansu ya rasu
- Abdullahi Abacha, da na kusa da karshe ga tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya Sani Abacha, ya rasu yana da shekaru 36
- Majiya daga iyalan sun ce za a yi jana'izar Abdullahi a masallacin kasa da ke Abuja, ranar Asabar, 4 ga watan Maris
FCT, Abuja - Abdullahi Abacha, daya cikin yayan tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, marigayi Janar Sani Abacha, ya rasu yana da shekaru 36, Daily Nigerian ta rahoto.
An rahoto cewa majiyoyi daga iyalan sun ambato Abdullahi ya rasu cikin barcinsa a gidansu da ke layin Nelson Mandela da ke Abuja.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An ambato majiyar na cewa:
"Lafiyarsa kalau kuma ba abin da ke damunsa daren jiya amma an gano ya rasu da safiyar yau. Ya rasu cikin barcinsa."
Za a yi jana'izarsa misalin karfe 4 na yamma a masallaci na kasa da ke Abuja, ranar Asabar, 4 ga watan Maris.
An haife shi a shekarar 1986, marigayin na daya cikin 'ya'ya tara da marigayin shugaban mulkin sojan ya rasu ya bari.
Yan Najeriya, da dan uwan Abdullahi sun yi martani kan rasuwarsa.
Captain Jamil Abubakar, abokin marigayin ya yi rubutu a Twitter:
"Innalillahi wainnailaihirraju'un, mun rasa daya cikin abokin mu kuma aboki, Abdullahi Sani Abacha. Yana cikin aji na NMS97; a Delta Company ya ke. Ina mika ta'aziyya ga iyalansa, abokansa da abokan karatunsa."
Sadiq Abdulmumin ya rubuta:
"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun!
"Ina mika ta'aziyya ga iyalan Abacha. Allah madaukakin ya ba ku kwarin gwiwan jure wannan babban rashin. Allah ya saka wa Abdullahi Sani Abacha da aljanna firdausi ya kuma yafe masa zunubansa."
Politics Nigeria ta rahoto cewa dan uwansa, Mahmud Abacha, dan tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya na hudu, shima ya tabbatar da labarin mara dadi a wani wallafa da ya yi.
Ya rubuta:
"Yanzu na rasa dan uwa na, Abdullahi. Allah ya jikansa ya saka masa da Jannatil Firdausi."
Hakimin Basirka, Muhammad Suleiman, da yaransu 3 sun rasu a hadarin mota a Jigawa
A baya-bayan nan kun ji cewa dan Amar na masarautar Dutse kuma hakimin Basirka a Jihar Jigawa ya rasu.
Rahotanni sun ce basaraken ya rasu ne sakamakon hadarin mota a hanyar zuwa garin Gwaram tare da iyalansa.
Guda uku cikin yayansa sun rasu yayin da matarsa da sauran yara biyu sun jikkata.
Asali: Legit.ng