Jihohi 7 da Suka Bayyana Rashin Amincewarsu da Zaben Shugaban Kasa Sun Janye Karar da Suka Shigar
- Jihohi bakwai a Najeriya da suka maka gwamnatin Najeriya a kotun koli kan zaben 2023 sun bayyana janye karar da suka shigar
- Jihohin da suka bayyana kalubalantar Tinubu ta hanyar lauyoyinsu a baya sun hada Akwa Ibom, Bayelsa, Delta, Edo, Taraba da Sokoto
- Sun bayyana a baya cewa, sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi a ka tattara a jihohi 36 da FCT duk ba su inganta ba
Najeriya - A wani yanayi mai daukar hankali game da sakamakon zaben 2023, wasu jihohin da suka kalubalanci nasarar Tinubu sun janye karar da suka shigar a kotu.
Jihohin bakwai da gaba dayansu ke karkashin jam’iyyar PDP sun hada da Adamawa, Akwa Ibom, Bayelsa, Delta, Edo, Taraba da Sokoto.
A baya sun shigar da kara ne kan gwamnatin tarayya a gaba kotun koli, inda suka bayyana karara suna kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da aka sanar, rahoton jaridar Vanguard.
Zaben bana ya zo da liki
Idan baku manta ba, an sanar da sakamakon zaben shugaban kasa, inda aka ce Bola Ahmad Tinubu ne ya lashe zaben, Punch ta ruwaito.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sanarwar janyewa daga karar kalubalantar na dauke ne da sa hannun Mr. Mike Ozekhome SAN, kuma ta ce:
“Ku sani cewa mai shigar da kara ya yanke shawarin dakatar da karar kan wanda yake kara.”
Ana ci gaba da taya Tinubu murnar lashe zaben bana
A bangare guda, jiga-jigan siyasar Arewa na ci gaba da bayyana jin dadinsu ga yadda Bola Ahmad Tinubu ya yi nasara a zaben bana.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya ce ‘yan Najeriya sun yi zabin da zai kawo musu dauki a kasar.
Ya kuma bayyana cewa, yana da yakinin Tinubu ne zai ciyar da Najeriya gaba ta hanyar amfani da kwarewa da gogewarsa a fannin siyasa da rayuwa.
Kotu ta ba Atiku da Obi damar bincika sakamakon zabe
Yayin da aka kammala zabe, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP sun ce basu amince da sakamakon zaben ba.
Wannan yasa suka tafi kotu don samun daman yadda za su kalubalanci sakamakon zaben a gaba.
Kotu ta ce ta ba su damar su binciki takardun da aka yi amfani dasu a zaben na bana.
Asali: Legit.ng