Hukuncin da Kotun ƙoli ta Yanke Na Canjin Fasalin Kuɗi Shine Kyakkyawan Tushe Ga Mulkin Tinubu — Yahaya Bello
- Yau Kotun Ƙoli da Ake wa Laƙabi da Kotun-Daga-Ke-Sai-Allah-Ya-Isa Ta Cire Dokar Hana Amfanin Da Tsofaffin Kudi
- Gwamnonin jam'iyyar APC sun bayyana farin cikinsu game nasarar da suka samu kan gwamnatin tarayya
- Gwamnan jihar Kogi, wanda yana cikin wadanda suka shigar da gwamnati kara ya bayyana ra'ayinsa
Gwamna Yahaya Bello ya Bayyana Cewa Juma'ar Da Zatayi Kyau, Tun Daga Laraba Ake Ganewa, Saboda Haja Yan Najeriya Suyi Fatan Ganin Sabuwar Gwamnati da Kaɓakin Alkairi.
Yayin da Kotin ƙoli ta yanke hukuncin aka ƙarar wasu jihohi suka shigar na canja fasalin Naira. Masu sharhi da faɗa aji na cigaba da bayyana ra'ayin su akan wannan lamari mai jan hankali.
Ɗaya daga cikin sanannun mutane da suka tofa albarkacin bakinsu game da wannan lamari shine gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.
Gwamnan ya maida martani ne akan batun, jim kaɗan da yanke hukunci na ƙarshe yau a Abuja.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yahaya Bello yace, hukuncin da kotun ƙoli ta yanke alamune da suke nuna takun tubali mai kyau zai zamto fandishon na gwamnati mai zuwa
wanda zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Tinubu zai jagoranta.
Idan dai za'a iya tunawa, a ranar juma'a ɗin nan ne Kotun ƙoli ta cire takunkumin daina amfani tsofaffin kuɗi na ₦200, N500, ₦1000.
Kotun ta ƙoli, ta samu yanke hukuncin hakan ne a ƙarƙashin jagorancin wani kwamitin alƙalai guda bakwai.
Inda suka fitar da matsaya akan cewa, tsofaffin ƙudin za'a ci gaba da amfani da su wajeb siye da siyarwa daga nan har zuwa Disamba 31, na wannan shekara.
Jihohin dai da suka shigar da ƙara gamida nasara akan shari'ar sune Jihohin Kaduna, Kogi, Zamfara, Katsina, Lagos, Cross River, Ogun, Ekiti, Ondo, Sokoto, Rivers, Kano, Niger, Jigawa, Nasarawa, Plateau da kuma jihar Abia, rahoton jaridar Vanguard
Legit ta tattauna da wasu mazauna birnin tarayya inda Yahaya Bello yayi magana inda suka bayyana ra'ayoyinsu.
Hanif Taofeek a jami'ar Abuja ya bayyana cewa aikin banza kotu tayi saboda ai tuni bankuna sun kwace tsaffin kudaden daga hannun mutane.
A cewarsa:
"A bangare guda akwai dadi, amma kuma ina sauran tsaffin kudaden da aka yanke hukunci kai? duk suna asusun bankuna."
"CBN ta kwashe Tiriliyan biyu kuma ta buga N500b kadai."
Hussain daga Kubwa ya bayyana cewa wannan tsari na sauya fasalin kudi ya jefa dubban talakan marasa asusun banki cikin garari.
Ya ce Ubangiji ne mafi sani bisa wanna hali.
Boko Haram Sunyi Awon Gaba da Wasu Matafiya Guda 7
A wani labari daban, Ƴan kungiyar Jamā’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l Jihād wanda aka fi sani da Boko Haram sun ƙaddamar wa wasu matafiya harin bazata.
Mayakan masu iƙirarin yin jihadi, sun farmaki wasu matafiya ne a cikin Magumeri ta Barno, sannan suka yi awon gaba da 7 daga cikin matafiyan.
Asali: Legit.ng