'Yan Sanda Sun Gurfanar da Wani Mutum da Aka Kama da Hular Sata a Gaban Kotu
- Wani matashi ya gamu da fushin alkali bayan da aka kawo shi kotu bisa zargin sace kayan sakawa da huluna
- Wannan lamarin ya faru a Abuja, inda ‘yan sanda suka bayyana gaskiyar abin da ya faru a lamarin
- Bayan jin komai, matashin ya musanta zargin da ake masa, an dage ci gaba da sauraran karar zuwa 14 ga watan Maris
Abuja - An gurfanar da wani matashi dan kasuwa, Khalisu Ahmadu mai shekaru 20 a ranar Alhamis a kotun Dei-Dei da ke Abuja bisa zargin satan huluna ‘fez caps’ da kayan sakawa na N250,000.
‘Yan sanda sun gurfanar da Ahmadu ne da ke zaune a Angwa Danladi, Zuba bisa zarginsa da aikata ta’addancin ketare gida da kuma tafka sata, Daily Trust ta ruwaito.
Dan sanda mai gabatar da kara, Olanipekun Babajide ya shaidawa kotu cewa, an kawo karar matashin ne a ofishin ‘yan sanda a ranar 12 ga watan Faburairu cewa a ranar 5 ga watan ya shiga wani gida.
Yadda ya yi satar
A cewarsa, ana zargin matashin ne da shiga gidan wani mutum Abdulrahman Dauda da ke Fruits Market, Dakwa a Abuja tare da sace kaya da hulunan da suka kai N250,000.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya kuma bayyana cewa, a ranar 12 ga watan Faburairu, Abdulrahman ya kawo barawon tare da mika shi ga ‘yan sanda.
A lokacin da bincike ya yi zurfi, wanda ake zargin ya gaza ba da bayanai masu kama hankali game da karan kansa.
Dan sanda mai gabatar da kara ya ce, laifin ya saba da sashe na 79, 348 da 288 na kundin Panel Code, African News Agency ta tattaro.
Ban aikata ba, inji wanda ake zargi
Sai dai, da aka je gaban alkali, wanda ake zargi ya musanta zargin da ake kansa.
Mai shari’a Malam Saminu Suleiman ya ba da belin wanda ake zargin a kan kudi N100,000 tare da kawo mutum daya da zai tsaya masa.
Hakazalika, mai shari’a ya dage ci gaba da zama kan batun har zuwa ranar 14 ga watan Maris.
A wani labarin, kunji yadda aka gurfanar da wani barawon da ake zargi da lallabawa tare da yunkirin sace janaretan kotu.
Asali: Legit.ng