"A Cigaba Da Amfani Da Tsaffin Kudi Har Karshen Shekara": Kotun Kolin Najeriya Ta Yanke Hukunci

"A Cigaba Da Amfani Da Tsaffin Kudi Har Karshen Shekara": Kotun Kolin Najeriya Ta Yanke Hukunci

  • Kotu mafi girma a Najeriya ta cika alkawarinta na kare zama kan lamarin sauya fasalin Naira
  • Bayan zamanta na karshe ranar 22 ga watan Febrairu, kotu tace ranar Juma'a zata yanke hukunci
  • Kotun ta watsawa gwamnatin shugaba Buhari kasa a ido a ittifakin da Alkalanta bakwai suka yi

Abuja - Kotun kolin Najeriya ta yanke hukuncin cewa yan Najeriya su cigaba da amfani da tsaffin takardun Naira har zuwa karshen shekarar nan.

Kotun ta caccaki tsarin daina amfani da tsaffin takardun Naira da gwamnatin tarayya da babban bankin Najeriya CBN ta kawo, rahoton Leadership.

Wadannan kudi sun hada da N200, N500 da N1000.

Kotun ta bayyana hakan ne ranar Juma'a yayin yanke hukunci kan karar da wasu jihohi uku suka shiga kan gwamnatin tarayya.

Alkalan kotun guda bakwai sun yi watsi da dukkan hujjojin Antoni Janar kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami.

Kara karanta wannan

Muje zuwa: Sanata ya fadi wulakacin da gwamnan CBN zai gani bayan saukar Buhari

Kotun Koli
Kotun Kolin Najeriya Ta Yanke Hukunci Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Alkali Emmanuel Agim, wanda ya karanta hukuncin ya bayyana cewa hujjojin da Antoni Janar, gwamnatin jihar Bayelsa da Edo suka gabatar cewa kotun koli ba tada hurumin sauraron karar an yi watsi da su.

A bisa sashe na 23(2) 1 na kundin tsarin mulkin Najeriya a cewar kotun, tana da hurumin shiga tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi, riwayar ChannelsTV.

Kotun ta kara da cewa wannan doka ta sauyin fasalin kudi ta jefa yan Najeriya cikin halin kunci da garari kuma Shugaba Buhari ya saba umurnin da tayi.

Alkali Agim ya cewa Buhari bai nemi shawarin majalisar magabatan kasa ba sai da ya aiwatar da dokar kuma ya take hakkin yan Najeriya.

Su wanene suka shigar da gwamnati kara kotun koli

Jihohin tarayya guda goma sha shida (16) suka shigar da gwamnatin tarayya kara kotun koli kan rashin halascin haramta tsaffin takardun kudin N1000, N500 da N200.

Kara karanta wannan

Naira: El-Rufa'i Da Yahya Bello Sun Dira Kotun Koli Inda Za'a Yanke Hukunci Yanzu

Gwamnonin Kaduna, Kogi da Zamfara ne suka fara shigar da wannan kara.

Daga bisani gwamnoni goma sha uku suka bi sahunsu. Sun hada Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers, dss.

Ra'ayin masana game da wannan shari'a

Legit ta tattauna da Assc Farfesa Murtada Ahmad, malami a jami'a Nile dake birnin tarayya Abuja inda ya yi kira ga shugaban kasan ya bi umurnin kotu idan yana son zaman lafiya.

A cewarsa, idan bai bi umurnin kotu ba, ya tuna ba zai dawwama kan mulki ba, wata rana zai bukaci kotu.

A cewarsa:

"Gwamma ya girmama doka saboda nan ba da dadewa ba zai yi hannun riga da mulki. Shima dai zai iya bukatan kotu a nan gaba."

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida