An Dakatar da Shugaban APC a Jihar Neja Saboda Ya Kadawa Atiku Kuri’a
- Jam’iyyar APC a jihar Neja ta dakatar da wani shugabanta bisa nemawa PDP kuri’u da kuma zaben jam’iyyar a zaben da ya gabata
- Jam’iyyar ta bayyana tuhume-tuhume da kuma yadda ta gano ya ci dunduniyarta a zaben 25 ga watan Faburairu
- An kammala zaben shugaban kasa a Najeriya, Bola Ahmad Tinubu ne ya lashe zaben da kuri’u masu yawan gaske
Jihar Neja - Shugaban jam’iyyar APC a jihar Neja, Haliru Zakari Jikantoro ya sha dakatarwar jam’iyyar bisa zargin cin dunduniyar jam’iyya.
Wannan na kunshe ne a cikin wasika mai dauke da kwanan watan 2 ga watan Maris 2023 dauke da sa hannun shugaba da sakataren gundumar Kashini a karamar hukumar Agwara, Amadu Abdullahi Yagode da Nuruddeen Abdullahi.
Hakazalika, wasikar na dauke da amincewar manyan jiga-jigai 21 na jam’iyyar a gundunar da ke tuhumarsa da zaban jam’iyyar PDP a zaben ranar Asabar.
Idan baku manta ba, Atiku Abubakar ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata na 25 ga watan Faburairu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Abin da ya faru tsakanin jam’iyyar da shugabanta
A cewar wani bangare na sanarwar:
“Akwai a rubuce cewa, Hon. Haliru Zakari Jikantoro ya ci dunduniyar jam’iyya ta hanyar sama wa jam’iyyar PDP kuri’u a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya.
“Babu mamaki yadda a lokacin da babban zabe ya karato Hon. Haliru bai tuntuba ko kira wani taro da jiga-jigan gunduna ko karamar hukumar ba don sanin matakin shirinsa a zaben da ke tafe.
“A madadin haka, Hon. Haliru ya kasance yana amfani da kudinsa wajen daukar nauyin kamfen PDP da kuma nemawa PDP kuri’u a karamar hukumar Agwara.”
An so jin ta bakin shugaban jam’iyyar a matakin karamar hukuma, amma hakan bai samu ba.
An kira wayarsa bai amsa ba, haka kuma bai mayar da sakon tes da aka tura masa ba.
Mu hadu a kotun, wa ke tsoro, inji APC ga Peter Obi
A wani labarin kuma, kun ji yadda jam’iyyar APC ta bayyana matsayarta kan martanin Peter Obi na cewa zai kalubalanci sakamakon zaben bana.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake taya Bola Ahmad Tinubu murnar lashe zaben shugaban kasa.
Peter Obi ya ce shi ne ya lashe zabe a 2023, don haka yana bukatar a bashi hakkinsa kamar ya doka ta tanada.
Asali: Legit.ng