"Zamu Fara Gina Ƙonanniyar Kasuwar Maiduguri Ta Monday Market Daga Makon Nan" - Zulum

"Zamu Fara Gina Ƙonanniyar Kasuwar Maiduguri Ta Monday Market Daga Makon Nan" - Zulum

  • Duk da Cewa Baya Gari Lokacin da Gobarar ta Faru, Yana Dawowa Ya Zarce Wajen Kai Tsaye
  • Gwamna Zulum Ya Kafa Kwamiti Domin Soma Aikin Kasuwar A Satin Nan da Muke Ciki.
  • Yayin da Ake Jiran Agaji Daga Gwamnatin Tarayya, Shugaban Tetfund Mutawali Kashim Ibrahim Ya Bada Tallafin ₦100,000,000.

Abuja - A ranar Litinin ɗin nan data gabata ne mutanen Maiduguri suka haɗu da wani iftila'in gobara a kasuwar "Monday Market"

Gobarar data data tashi cikin dare, anta dauki ba dadi da ita har wajen 8:30 na safe, kuma tabar baya da ƙura, inda ta janyo asarar dukiya maɗuɗai da kadarori marasa ƙirguwa.

A wani yunƙuri da gwamnatin jihar take don ganin ta ragewa wa masu shaguna raɗaɗi a ƙarƙashin jagorancin gwabnan jihar ta Maiduguri, Farfesa Babagana Ummara Zulum ta bada umarnin sake fara gina kasuwar nan take ba tare da ɓata lokaci ba.

Kara karanta wannan

Matasa Sun Tare Motar Shinkafa a Zaria, Sun Ɗebe Buhu 29

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zulum
Za'a Soma Sake Gina Ƙonanniyar Kasuwar Maiduguri Ta Monday Market A Satin Nan - Zulum Hoto: Twitter/GovBorno
Asali: Twitter

Gwamnan ya sanar da haka ne a yayin amsar ziyarar jajantawa ga gwamnatin Borno da wasu sanannun mutanen Borno da Sanata Babagana Kingibe ya jagoranta a Abuja.

Anyi ittifaƙin cewa, kasuwar ta "Monday Market" kasuwa ce mai daɗaɗɗen tarihi da takai kimanin shekaru 40 da kafuwa.

Inda masu siye da siyarwa daga ko ina na faɗin Afirka da duniya ke zuwa haɗa hada-hada.

Kasuwar kuma itace kasuwa mafi girma a Arewa Maso Gabashin Najeriya gabaki ɗaya kwata.

Da yake zantawa da baƙin, Zulum yace:

"Mun haɗa kwamati da zai gudanar da al'amuran Kasuwar "Monday Market", Kwamitin zaiyi aiki domin gyara duka shagunan da aka ƙone. Insha Allah gobe Kwamitin zai soma aiki".

Zulum ya ƙara da cewa:

"Yayin da muke jiran tallafi daga gwamnatin tarayya, ba zamu riƙe hannayen mu ba bamuyi komai ba, dole ne mu soma da namu ƙoƙarin". Inji Zulum.

Kara karanta wannan

Duniya Rawar Ƴan Mata: Lalong Ya Tunkuyi Ƙasa a Takarar da Yayi Ta Sanata

Gwabnan Zulum ya miƙa godiya ga baƙin da suka haɗa da manajan daraktan NNPC Kolo Mele Kyari, Shugaba Tetfund Mutawali Kashim Ibrahim da sauran manyan baƙi.

Da yake nashi jawabin, shugaban tawagar masu ziyarar, Ambasada Kingibe ya jajantawa masu shagunan da suka samu ibtilain ne.

Sannan ya yabawa ƙoƙarin gwamnatin Zulum wajen taimakawa mutanen da abin ya shafa.

Inda yake cewa:

"Muna godiya tare da yaba yadda mai girma Gwamna kayi tallafi da ɗaukar matakin gaggawa. Muna sane baka gari sanda abin ya faru, amma daka dawo ka wuce kai tsaye zuwa wajen. Kayi magana akan abu, sannan ka kafa kwamiti , domin dubo irin barnar da aka tafka". Inji Kingibe.

Daga ƙarshe kuma, Shugaban hukumar Tetfund, Mutawali Kashim Ibrahim ya bada tallafin miliyan ₦100 domin a tallafawa waɗanda iftila'in ya rutsa dasu.

Kwamitin Kamfen Atiku Ya Yi Kira Ga INEC

Kara karanta wannan

A Kwantar Da Hankali, Kada a Kaiwa Igbo Hari, Inji Tinubu akan Rashin Nasararsa a Legos

Kwamitin yakin neman shugaban ƙasa na jam'iyyar adawa ta PDP ya yi kira ga INEC da ta soke dukkan sakamakon da aka sanar kawo yanzu.

Hakan ya fito ne ta bakin nai magana da yawun kamfen din takarar ta Atiku, Daniel Bwala wanda hay bayyana hakan a jawabin da ya fitar ranar Talata, rahoton ChannelsTV wanda Jaridar Legit ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida