Tirƙashi: Matasa Sun Tare Mota Cike Da Hatsi Tare da Ɗebe Buhu 29 Akan Hanyar Zuwa Zariya
- Motar Cike da Damman Buhhunan Hatsi Ta Tunkari Zariya ne Lokacin da Sukayi Mata Kwantan Ɓauna
- Sun Mata Dirar Mikiya Tare Da Ƙoƙarin Sace Buhu 29 da Suke Ciki Inda Zakara Bai Basu Sa'a Ba
- Jami'an Kan-Kace-Kwabo na Hukumar Civil Defence Sun Dira Wajen Tare Da Kama Su Da Kubutar da Direba da Yaron sa Lafiya Kalau.
Duniya ina zaki damu ne wai. A lokuta da dama mutane kan aikata ayyukan da ke sanya su yin dana sani yayin da suka shiga hannu ko kuma sukai ƙoƙarin tuba.
A wannan gwadaben, irin mutanen nan da suke aikata dana sanin ne suka ƙara shiga hannun zaratan jami'an tsaro na Civil Defence.
Domin kuwa wasu matasa 19 ne suka shiga hannun Hukumar Tsaron Farar Hular na Civil Defence suna tsaka da aikata masha'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamun ya samo asalin ne biyo bayan zargin matasan da ake da sibaran-nabayye buhhunan shinkafa da wata mota ke ɗauke dasu don kaiwa zuwa birni Zazzau.
Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar Tsaron Farar Hula na Sibil defens mai suna DSC Ibrahim Idris-Abdullahi ne ya bayyana kamun a ranar Litinin ɗin data gabata ga jaridar Daily Trust.
Kamar yadda ya faɗa, matasan da ake zargi sun farmaki motar ne tana tsaka da tafiya akan titin Kano-Zariya.
Jami'in yace motar tana ɗauke da lambar mota mai alamar UGG 532 XA, kuma a tattare da ita a cike take da buhhunan shinkafa mai nauyin 50Kg daga kamfanin sarrafa shinkafa na Alhamsad dake sharaɗan Kano.
A cewar sa:
"Mun samu rahoton ujila akan harin, inda bamuyi wata wata ba jami'an mu na kan kace kwabo sukayi wa wajen dirar mikiya, tare da kama ɓarayin da ake zargi, nan take kuma muka ƙwato buhhunan shinkafa da suke shirin sacewa har guda 29.
"Matuƙin da shi da yaron sa mun samu nasarar amso su, batare da an musu koda ƙwarzane ba," Inji Idris-Abdullahi.
Daga ƙarshe mai magana da yawun hukumar ya tabbatar da cewa, waɗanda ake zargin, za'a gurfanar da su a gaban kotu domin girbar abinda suka aikata idan har aka gama tattara bayanai akan su.
A wani labari na daban kuma kunji yadda wani ɗan Achaɓa yayi nasarar zama ɗan majalisa a Kaduna kuwa?
Yadda Wani Ɗan Acaɓa Ya Samu Nasarar Zama Ɗan Majalisa a Kaduna
Jaridar Legit ta ruwaito yadda wani mutum mai suna Mr Donatus Mathew ya zama ɗan Majalisar Kaura dake jihar Kaduna.
Hakan ya biyo bayan zaɓen da aka gudanar na ranar asabar ne, kamar yadda baturen zaɓe ya sanar da lashe zaɓen da yayi na gundumar Kaura dake jihar Kaduna.
Da baturen zaɓen yake sanar da lashe zaɓen na ɗan Acaɓar, Farfesa Elijah Ella yace Mathew ya samu adadin ƙuriu guda 10,508 cicif.
Wanda hakan ya bashi dama domin hamɓarar da mai wakiltar Kauran a majalisar tarayya a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP wato Gideon Lucas Gwani wanda yazo na biyu da adadin ƙuriu 10, 297.
Asali: Legit.ng