Peter Obi Ya Lallasa Tinubu, Atiku da Kwankwaso A Birnin Tarayya Abuja
- Tsohon gwamna Peter Obi na jam'iyyar Labour Party ya zama zakaan gwajin dafi a siyasar Najeriya
- Ya yiwa Asiwaju Tinubu na APC da Atiku Abubakar na PDP babban lahani a zaben dake gudana
- Har yanzu ana cigaba da tattaro sakamakon zabe daga kananan hukumomi da jihohi a fadin tarayya
Abuja - Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Gregory Obi, ya samu nasara a zaben babbar birnin tarayya FCT Abuja.
Nasarar Obi ta bayyana ne bayan kammala kirgen kuri'u a manyan hukumomin Abuja guda shida, rahoton TheCable.
Ya lallasa Asiwaju Bola Tinubu na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Atiku Abubakar na jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, da Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party NNPP.
Zaku tun cewa jam'iyyar PDP ce ta shahara da lashe zabe a Abuja, amma wannan karon na uku ta zo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ga Sakamakon:
APC: 90,902
PDP: 74,199
LP: 281,717
NNPP: 13,247
Adadin wadanda aka tantance: 478923
Halastattun kuri'u: 460080
Kuri'un da aka watsar: 18581
Ga yadda zaben ya kaya a kananan hukumomi Abuja
1. Gwagwalada Area Council
APC— 15890
LP— 19,694
NNPP— 483
PDP— 10987
2. Bwari Area Council
APC 13156
LP 67,198
NNPP 877
PDP 10835
3. Kuje Area Council
APC 10648
LP 14,257
NNPP 266
PDP 10028
4. Abaji Area Council
APC 10370
LP 2874
NNPP 104
PDP 6888
5. Kwali Area Council
APC 11,242
LP 7,302
NNPP 324
PDP 9,054
6. AMAC
APC 29596
LP 170392
PDP 26407
Lalong Ya Gaza Samun Nasarar Kujerar Sanata Da Ya Nema
Babban Darakta janar na yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shettima kuma gwamnan Jihar Plateau Simon Lalong shima yasha ƙasa a ƙoƙarin sa na zuwa majalisar dattawan Najeriya.
Da Dumi-Dumi: Dan El-Rufai Ya Kayar Da PDP, NNPP Da Sauran Yan Takara, Ya Lashe Kujerar Majalisar Tarayya
Lalong yasha kayi ne a hannun ɗan takarar jam'iyyar PDP mai suna Napoleon Bali.
Jaridar Vanguard ta ambato cewa Lalong yayi takara a cikin inuwar jam'iyyar APC kuma ya samu ƙuria guda 91, 674, yayin da Bali wanda yayi nasara ya samu ƙuri'u 148,844.
Idan dai za'a iya tunawa, tun a tashin farko me dai, Lalong ya rasa akwatin sa dake Ajikamai ga jam'iyyar Labor Party da kuma Shendam ta tazara mai matuƙar yawa.
Asali: Legit.ng