Sanata Ibn Na’Allah Ya Yi Rasa Kujearsa Ta Sanata, Dan PDP ya Kwace
- Sanata Bala Ibn Na'Allah ya rasa kujerarsa ta sanata, inda dan takarar jam'iyyar PDP ya samu nasarar kujerar
- Sanata Na'Allah ya rike kujerar sanata har sau uku, ya kuma rike ta majalisar wakilai har sau biyu
- Ana ci gaba shigo da sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya a fannoni daban-daban na kasar nan
Jihar Kebbi - Sanata Bala Ibn Na'Allah ya rasa kujerarsa ta sanata a mazabar Kebbi ta Kudu a zaben ranar Asabar 25 ga watan Faburairu.
Garba Musa Maidoki, dan takarar jam'iyyar PDP a mazabar ne ya lashe zaben da aka yi a karshen makon jiya, Daily Trust ta ruwaito.
Baturen zaben jihar, Farfesa Ibrahim Muhammad ya sanar da sakamakon zaben da cewa, dan takarar na PDP ya samu kuri'u 75,232 yayin da Na'Allah ya samu 70,785.
Na'Allah ya kasance a majalisar dattawa har sau uku, kana ya shafe majalisar wakilai ta tarayya sau biyu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya rasa kujerarsa ne ga dan takarar PDP da wannan ne karonsa na farko na takara da akalla kuri'u 5000.
Rikici bayan zaben 2023 a jihar Kebbi
A bangare guda, wasu mabiya jam'iyyun siyasa a jihar Kebbi sun rike wasu jami'an zabe a mazabar sanata Kebbi ta tsakiya kan sakamakon zabe.
'Yan a mutun jam'iyyun suna ta zanga-zangar jinkirin sanar da sakamakon zaben sanatan yankin tsakanin gwamna Abubakar Atiku Bagudu da Adamu Aliero.
Bayan ganawa da sanata Aliero da dan takarar gwamnan jihar, Janar Aminu Bande (mai ritaya), sun toshe mashiga filin tattara zabe na jihar Kebbi, 21st Century Chronicle ta ruwaito.
An farmaki wani jami'in INEC da ya sha dakyar, wanda rahoto yace an fitar dashi daga wurin dakyar.
Hakazalika, 'yan jaridar da ke daukar hotunan abin da ya faru a wurin, amma an samu daukin jami'an tsaro.
Oshiomole ya zama sanata
A wani labarin kuma, kun ji yadda Adams Oshiomole ya lashe kujerar sanata a jihar Edo da ke Kudancin kasar nan.
Wannan lamari ya zo ne a daidai lokacin da aka kirga kuri'u kuma jami'in INEC ya sanar da wanda ya lashe zabe.
Asali: Legit.ng