'Yan Sanda Sun Cafke Lakcara Ɗauke Da Na'urorin Tantance Masu Kaɗa Ƙuri'a
- Ƴan sanda sun yi babban kamu, sun cafke wani matashi ɗauke da na'urar tantance masu kaɗa ƙuri'a
- Matashin yayi sojan gona ga jami'in tattara sakamakon zaɓe na hukumar zaɓe ta INEC a jihar Cross Rivers
- Tuni jami'an hukumar ƴan sanda suka tasa ƙeyar sa domin cigaba da samun muhimman bayanai daga wajen sa
Cross Rivers- Hukumar ƴan sanda ta cafke wani matashi ɗauke da na'urar tantance masu kaɗa ƙuri'a (BVAS), a jihar Cross River.
Matashin mai suna Gabriel Agabi, an cafke shi da na'urorin guda 17 ne a wata mazaɓa wacce ba domin nan aka yo na'urorin ba. Rahoton Channels Tv
Mr Agabi, wanda yake sanye da rigar hukumar zaɓe ta INEC, ya shiga hannun ƴan sanda ne a cibiyar tattara sakamakon zaɓe ta Okpoma, a ƙaramar hukumar Yala ta jijar Cross Rivers.
Matashin da ake zargi da yin sojan gona yayi iƙirarin cewa shi lakcara ne jami'ar Calabar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tuni dai ya fitar da wasu bayanai ga ƴan sanda waɗanda suka tasa ƙeyar sa zuwa ofishin ƴan sanda na Ogoja, domin cigaba da tatsar bayanai a hannun sa.
Agabi wanda ya fito daga Ugoro a ƙaramar hukumar Bekwarra a jihar, yayi sojan gona ne ga Dominci Abekadi, jami'in tattara zaɓe na hukumar INEC a mazaɓar Yache, cikin ƙaramar hukumar Yala ta jihar.
Ɗaya daga cikin na'urar BVAS ɗin da aka same shi da ita tana ɗauke da sunan “BVAS No: 09/18/10/012 inda aka tantance masu kaɗa ƙuri'a 216 sannan mutum 250 suka kaɗa ƙuri'a. Rahoton Premium Times
Sojan gonar wanda ake zargin yana yiwa wata jam'iyya aiki ne, ya haɗa kai da wasu ɓata gari inda ya kulle wakilan sauran jam'iyyun.
Yayi ɓatan dabo tun lokacin da aka kammala zaɓe da misalin ƙarfe 6 na yamma a raanr Asabar, inda ba a sake ganin sa ba sai a cibiyar tattara sakamakon zaɓe ta Ogoja da misalin ƙarfe 5 na yamma a ranar Lahadi.
Wani babban jami'in ɗan sanda da ya nemi a sakaya sunan sa, wanda yake a wajen ya tabbatar da aukuwar lamarin.
A wani labarin ma daban kuma, gwamnatin El-Rufai ta haramta zanga-zanga a faɗin jihar Kaduna.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar shine ya tabbatar da hakan.
Asali: Legit.ng