Solomon Dalung Ya Sha Kaye a Mazabarsa, PDP Ta Lashe Zabe
- Solomon Dalung, tsohon minista a Najeriya ya sha kaye a zaben majalisar dokokin tarayya da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata
- Mrs Beni Lar ce ta lashe zaben da adadin kuri'u masu yawa, kuma wannan ne karo na biyar da za ta ci gaba da zama a kujerar
- Dalung, wanda ya tsaya takara a jam'iyyar SDP ya zo na uku a zaben, inda dan takarar APC ya zo na uku
Jihar Filato - Tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung ya fadi a zaben majalisar wakilai da aka gudanar a mazabarsa a ranar Asabar.
Dalung ya samu kuri'u 3,369 kacal a matsayinsa na dan takarar jam'iyyar SDP, inda ya zo na uku a jerin 'yan takarar majalisar tarayya a mazabar Langtang North/Langtang South.
Wacce ta lashe zaben, Beni Lar 'yar jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 42,008, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.
Ba wannan ne farkon lashe zabenta ba
Bayan lashe zaben, Mrs Beni Lar za ta ci gaba da zama 'yar majalisar yankin a karo na biyar kenan.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Na biyu a mazabar, Vincent Bulus na jam'iyyar APC mai mulki ya samu kuri'u 21,345.
Dalung dai ya kasance daya daga cikin ministocin da Buhari ya tsige a mulkinsa saboda wasu dalilai.
Bayan haka, ya fita daga APC tare da sukar yadda gwamnatin jam'iyyar ke tafiyar da lamuranta yadda a tunaninsa yace bai dace ba.
Sakamako dai na ci gaba da fitowa, jiga-jigai da yawa a kasar nan sun rasa kujerunsu na siyasa da suka dade suna rike dasu a zaben bana.
Na'Allah ya rasa kujerarsa ta sanatan Kebbi
A wani labarin kuma, sanata Bala Ibn Na'Allah ya ci taliyar karshe a majalisar dattawan Najeriya, dan takarar jam'iyyar PDP ya lashe zaben da aka yi.
An sanar da cewa, Bala Na'Allah zai zauna a gida na tsawon shekaru bayan da wani sabon dan takarar PDP ya kawo kuri'u mafi rinjaye a zaben na bana.
Na'Allah ya rike mukamin sanatan Kebbi ta har tsawon shekaru 12 kafin a yi waje dashi a wannan zaben na bana.
Asali: Legit.ng