Tsohon Gwamna Oshiomhole Ya Lashe Zaben Sanatan Edo Ta Arewa
- Tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa ya lashe zaben sanata a mazabar Edo ta Arewa a Kudancin Najeriya
- Adams Oshiomole ya samu kuri'u da yawa, inda ya banke abokan hamayyarsa a jam'iyyar PDP da sauran jam'iyyu
- Ana ci gaba da fito da sakamakon zabe a yankuna daban-daban na Najeriya tun bayan kammala zabe a ranar Asabar
Jihar Edo - Adams Oshiomole, tsohon gwamnan jihar Edo kuma tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa ya lashe kujerar sanata a Edo ta Arewa
Oshionole ya samu kuri'u 107,110, inda ya banke abokin hamayyarsa Francis Alimikhena na jam'iyyar PDP, Sahara Reporters ta tattaro.
Alimikhena ya samu kuri'u 55,344.
Hukumar INEC ta sanar da Oshiomole ne ya lashe zabe
Benjamin Adesina, baturen zabe a jihar Edo ya sanar da cewa, dan takarar da ya lashe zabe a mazabar Edo ta Arewa dai ba kowa bane face Oshiomole.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa:
“Adams Oshiomole na APC, ya samu kuri'u mafi rinjaye a zaben, don haka shi ne dan takarar da ya lashe zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Faburairu a mazabar sanata ta Edo ta Arewa.
Adams Oshiomole ya kasance daya daga cikin masu fada a ji a jam'iyyar APC mai mulki, kuma ya yi gwamna a Edo a shekarun baya da suka shude.
A lokacin da yake shugaban APC ne aka kafa gwamnatin Buhari, kuma tasirinsa ya shafi bangarori daban-daban na siyasar jam'iyyar.
Sanata Bala Ibn Na'Allah ya rasa kujerarsa ta sanata
A wani labarin kuma, jigon APC mai fada a ji ya rasa damar zama sanata a zaben 2023 na 'yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata 25 ga watan Faburairu.
Rahoton da muka samo ya bayyana cewa, dan takarar sanata a PDP ne ya yi nasarar karbe kujerar a hannun Sanata Bala, wanda ya dade yana rike da ita.
A cewar rahoton, Bala ya kasance sanata har sau biyu a mazabarsa da ke Kebbi, inda kuma ya kasance dan majalisar wakilai a matakin tarayya na tsawon zango biyu a jihar ta Kebbi.
Asali: Legit.ng