Hankula Sun Tashi Yayin Da Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallacin Juma'a, Sun Kashe 2, Sun Sace Da Dama A Niger

Hankula Sun Tashi Yayin Da Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallacin Juma'a, Sun Kashe 2, Sun Sace Da Dama A Niger

Jihar Niger - Yan bindiga sun kashe mutane biyu sannan sun sace wasu da dama a jihar Niger, Vanguard ta rahoto.

Wadanda aka sace din suna tafiya ne cikin babbanr mota suna hanyarsu na dawowa daga kasuwar Juma'a a karamar hukumar Rafi ta jihar.

Taswirar Niger
Taswirar Jihar Neja da ke arewacin Najeriya. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

An kuma rahoto cewa yan bindigan sun cinna wa babban motar wuta bayan sace fasinjojin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda aka sace sun hada da: maza, mata da yara.

Ba a san inda aka kai wadanda aka sace din ba a lokacin hada wannan rahoton.

Lamarin ya faru ne a Tashar Amale a karamar hukumar Rafi na jihar Niger.

Yan bindiga sun kutsa masallaci sun bindige masallata a Niger

Vanguard ta tattaro cewa baya da kisa da kuma sace fasinjojin, yan bindigan sun kuma kutsa wani masallaci sun tarwatsa sallar Juma'a da ake yi.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan daba sun sa wuta a hedkwatar hukumar INEC a wata jihar Arewa

Wasu daga cikin masallatan sun yi rauni sakamakon harsashin bindiga.

An kuma ce yan bindigan sun kai hari a wasu garuruwa da unguwanni da ke yankin inda suka rika harbin duk wanda suka hadu da shi, yan kauyen sun rika tsere wa amma sun bindige biyu.

Sakataren gwamnatin jihar Niger, Alhaji Ahmed Ibrahim Matane ya tabbatar da afkuwar lamarin amma ya ce ba a riga an tabbatar da adadin wadanda yan bindigan suka sace ba.

SSG din ya ce:

"Tabbas an kai hari kuma an sace fasinjoji amma ba mu riga mu tantance adadin wadanda aka kashe ba da wadanda aka sace."

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164