A Karon Farko, Peter Obi Ya Samu Nasarar Lashe Zabe a Karamar Hukumar Suleja Ta Neja
- Hukumar zabe ta ce, Peter Obi ne ya fi yawan kuri'u a karamar hukumar Suleja ta jihar Neja a Arewacin Najeriya
- Wannan na zuwa ne bayan da aka kirga kuri'un da al'ummar yankin suka kada a zaben shugaban kasa
- Ana ci gaba da kirgan kuri'u, jam'iyyar Labour na samun rabonta a zaben da aka yi shugaban kasa
Suleja, jihar Neja - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi ya lallasa abokan hamayyarsa a karamar hukumar Suleja a jihar Neja.
Suleja dai wani gari ne da ke kusa da Abuja, kuma yanki ne mai babbar kasuwa da ake ji da ita a yankin, Daily Trust ta ruwaito.
Sakamakon zaben shugaban kasa da hukumar zabe ta fitar a gundumomi 10 na karamar hukumar ya nuna cewa, Obi ya samu 16,978, yayin da Tinubu ya samu 15,917 sai kuma Atiku mai kuri’u 11,968.
Baturen zaben yankin, Dr. Hussaini Musa ne ya bayyana hakan a wurin sanar da sakamakon zaben a jihar Neja.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Suleja da yadda zabe ya kasance a cikinta
Karamar hukumar Suleja kadai na da gundumomi 10, kuma tana da mutum 149,088 da suka yanki katin zabe, an tantance mutum 50,358 a ranar zabe.
Mutum 49,850 ne suka kada kuri’unsu, inda aka samu sahihan kuri’u 42,028 sai kuma mutum 1,822 da suka yi kuskuren kada kuri’a.
A bangare guda, jam’iyyar APC ce ta lashe kujerar sanata a Neja ta gabas da kuri’u 18,805. Jam’iyyar PDP ce ta zo na biyu da kuri’u 14,525 LP kuma ta samu 13,407.
Har yanzu ana ci gaba da kirg kur'un da aka kada a zaben 2023 na shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya.
Jam'iyyar Peter Obi ta samu kujerar majalisar wakilai
A wani labarin kuma, kunji yadda dan takarar jam'iyyar Labour a majalisar wakilai a jihar Abia ya lashe zaben da aka yi a jiya Asabar.
Wannan na fitowa ne daga bakin baturen zabe, wanda yace dan takarar ne ya samu mafi yawan kuri'un da al'ummar yankin suka kada a ranar zabe.
Ya zuwa yanzu, jam'iyyar Labour na ci gaba da samun kuri'u a rumfunan zabe daban-daban na kasar nan.
Asali: Legit.ng