Yanzu-Yanzu: Fusatattun Matasa Sun Ƙaddamarwa Yar Jarida Tsaka da Ɗaukan Rahoton Gobarar Kasuwa a Borno
- Mumunar gobara ta ci dukiyar biliyoyi a babbar kasuwa dake birnin Maiduguri, jihar Borno
- Wata yar jarida da taje daukar rahoto a wajen gobarar ta game da fushin yan kasuwan da sukayi asarar dukiyarsu
- Mutane da dama sun bayyana ra'ayoyinsu game da wannan abu da fusatattun matasa suka yi
Maiduguri - A safiyar nan ta Lahadi ne aka tashi da wata masifaffiyar wuta data addabi sananniyar kasuwar nan ta"Monday Market" a garin Maiduguri.
Duk da masu ruwa da tsaki daga ɓangaren kawo agajin ujila domin kashe wuta suna ƙoƙarin shawo kan wutar amma abin ya gagari kundila (Misalin 1:00am-8:00).
Ana tsaka da ƙoƙarin kashe wutar ne sai kuma wasu fusatattun mutane suka ƙaddamar da hari akan Pauline Kuje Vana.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sakamakon Zabe: Tsoffin Gwamnoni da Ministoci, Sanatoci da Wasu Manya Sun Huro Wa INEC Wuta Kan Abu 1
Ita dai uwargida Pauline Kuje Vana maaikaciya ce ga babban gidan talabijin na ƙasa (NTA).
Kuma ita ce gidan talabijin ɗin yabawa alhakin kawo rahoto akan yadda gobarar take gudana a kasuwar ta jihar Barno.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewar, Kasuwar ta Monday market ta haɗu da iftila'in gobara ne tun karfe daya na dare wanda wutar bata tsaya ba sai aƙalla zuwa ƙarfe 8:30 na safe.
Duk wani ƙokari daya kamata ayi domin kashe gobarar, jami'an kashe gobara na Jihar Borno sunyi amma abin yaci tura.
Dalilin haka ne, wutar mai balbalin azabar yawa ta haddasa rasa dukiya maɗuɗai wanda bazasu lissafu da kuɗim Naira ba.
Ita dai yar jaridar an farmake tane tare da yi mata dukan tsiya ita da sauran abokan aikin ta yayin da tayi yunkurin aika rahoton yadda wutar ke ci ne kai tsaye.
Wani mai gani da ido ya shaidawa majiyar mu cewa:
" Fusatattun Mutanen sune masu shagunan, sun haɗa kai da masu yi musu jaje ne wajen ƙaddamar da harin ga mutanen dake haɗa rahoto, ta haka sai suka ji mata ciwo ita da mai kawo rahoton".
Tuni dai aka ɗauki mai rahoton zuwa ga Asibitin sojoji na 7 dake Maiduguri domin samun tallafin gaggawa.
A Wani Labari na daban ko kunji yadda wata mata ta yanke jiki a layin zabe ta fadi a zamfara kuwa?
Wata Mai Juna Biyu Ta Yanke Jiki, Ta Rasu a Kan Layin Zabe a Zamfara
Rahotanni daga jihar zamfara na nuni da yadda wata mata mai ɗauke da juna biyu, mai suna Shamsiya Ibrahim, ta yanke jiki ta faɗi yayin da take jiran layi ya zo kanta ta kaɗa kuri'a a yankin Tsafe, jihar Zamfara ranar Asabar.
Tunda fari dai, bayanai dun nuna cewar mamaciyar taso daga garin Kotorkwashi da ke yankin ƙaramar hukumar Bungudu zuwa Tsafe ne, tafiya mai nisan kilo mita 50, don kawai ta kaɗa kuri'arta.
Tana tsaka da bin layine ta yanke jiki ta faɗi a kan layin zaɓen, mutane sun yi hanzarin kai ta babban Asibitin Tsafe don ceto rayuwarta amma aka tabbatar rai ya yi halinsa daga isa.
Asali: Legit.ng