Gwamna Zulum Zai Tallafawa ’Yan Kasuwan da Gobara Ta Kone Shagunansu da N1bn

Gwamna Zulum Zai Tallafawa ’Yan Kasuwan da Gobara Ta Kone Shagunansu da N1bn

  • Gwamna Zulum na jihar Borno ya bayyana shirin ba da tallafi ga wadanda wata gobara ta shafa a jihar a jiya Asabar 25 ga watan Faburairu
  • Gwamnan ya ce ya ware Naira biliyan daya don tallafawa wadanda gobarar ta shafa, ya bayyana shirinsa na yadda za a raba tallafin
  • Ana yawan samun gobara a kasuwannin Najeriya, ba sabon abu bane gwamnatoci su tallafawa ‘yan kasuwan da gobarar ta shafa

Jihar Borno - Bayan aukuwar wata mummunar gobara a jihar Borno, gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ya yi bayani tare da alkawarin tallafawa wadanda shagunansu suka kone.

Gwamna Zulum ya bayyana cewa, zai ba da tallafin Naira biliyan daya ga ‘yan kasuwar da shagunansu suka kone a gobarar da ta faru.

Gwamnan ya fadi hakan ne a cikin wata sanarwar da ya fitar ta shafin Twitter ta hannun Isa Gusau, hadiminsa a fannin yada labarai.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali, Zaman Makoki Yayin Da Mata Da Miji Da Yaransu 6 Suka Rasu A Gobara A Zaria

Zulum zai tallafawa wadanda gobara ta taba a Maiduguri
Gwamna Babagana Umara Zulum | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Dalilin ba da tallafin ga al’ummar jihar Borno da gobara ta taba

A cewar sanarwar, tallafin zai taimakawa ‘yan kasuwan ne wajen rage radadi da asarar da suka yi na dukiyarsu a shagunansu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika, gwamnan ya ce idan ba a tallafawa ‘yan kasuwan ba, za su shiga wahalhalu a nan gaba.

A cewar Zulum, ya kafa kwamitin da zai duba wadanda suka tafka asara a gobarar don tabbatar da an taimakawa wadanda suka dace.

Za a dauki matakin faruwar hakan a gaba

A bangare guda, gwamna Zulum ya ce zai dauki matakin tabbatar an kar e faruwar irin wannnan gobarar mai jawo asara.

Ya kuma yi kira ga al’umma da su kwantar da hankali, tabbas gwamnati za ta tabbatar da an tallafawa wadanda abin ya shafa.

Idan baku manta ba, a jiya da dare ne gobara ta tashi a babbar kasuwar Maiduguri, ta ci dukiya mai yawan gaske.

Kara karanta wannan

Canza Kudi: Gwamnatin Buhari ta Fadi Irin Hukuncin da ke Jiran ‘Ganduje da El-Rufai’

Gobara ta tashi a wata kasuwar katako a jihar Anambra

A wani labarin na daban, wata mummunar gobara ta kone kayayyaki masu daraja a kasuwar katako da ke jihar Anambra a Kudancin Najeriya.

An ruwaito cewa, ba a rasa rai ba a gobarar, amma an yi mummunan asara ta dukiya a lokacin da wutar ta tashi cikin tsananin dare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.