Babu Bambanci Tsakanin Wasu ’Yan Siyasa Da ’Yan Fashi, Inji Tsohon Shugaba Jonathan
- Tsohon shugaban kasa a Najeriya ya siffanta ‘yan siyasan da ke siyan kuri’u da ‘yan fashi masu neman kudi ta hanyar sata
- Goodluck Jonathan ya kada kuri’arsa a jihar Bayelsa, ya yi jawabi game da zaben 2023 na shugaban kasa da aka yi
- Tsohon shugaban ya kuma yabawa INEC bisa kirkiro hanyar tantance kuri’u da na’urar BVAS da aka kawo a shekarar nan
Jihar Bayelsa - Tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan ya ce, ‘yan siyasan da ke amfani da tashin hankali ko siyan kuri’u basu da bambanci da ‘’yan fashi’.
Jonathan ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai bayan kada kuri’arsa a jihar Bayelsa da yammacin ranar Asabar 25 ga watan Faburairu, TheCable ta ruwaito.
Tsohon shugaban ya bayyana cewa, halin wasu ‘yan siyasan abin damuwa ne a lokutan zabe, inda ya ce kamata ya yi ake kallon siyasa a matsayin tsaftatacciyar sana’a.
A kalamansa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Fatana ga Najeriya shine a yi zabe cikin kwanciyar hankali.”
‘Yan fashi na neman kudi ta hanyar fashi, wasu ‘yan siyasa na neman kujera ta siyan kuri’a
Da yake buga misali, ya ce duk dan siyasan da ke amfani da karfin tashin hankali da siyan kuri’a wajen zama shugaba daidai yake da ‘yan fashi, Vanguard ta ruwaito.
Ya siffanta aikin irin wadannan ‘yan siyasan da cewa, ‘yan fashi na samun abin da suke so ne na kudi ta hanyar kudi, wasu ‘yan siyasan ma na samun kujera ne ta hanyar siyan kuri’u ko tashin hankali.
Ya kori ‘yan siyasa da su mai da hankali tare da bin doka da oda, a cewarsa:
“Bukatara ga ‘yan siyasa, hukumomin da tsaro da ma’aikatan INEC, shine su yi iyakar kokarinsuga kasar nan. Duniya gaba na kallonmu.”
Da yake magana kan kawo amfani da na’urar tantancewa ta BVAS, tsohon shugaban ya ce ci gaba ne mai kyau kuma abin a yaba.
An farmaki jami’an EFCC a jihar Imo da Abuja
A wani labarin, wasu ‘yan daba sun farmaki jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a babban birnin tarayya Abuja.
Hakan ya faru ne a lokacin da jami’an hukumar suka kama wani da ake zargin yana siyan kuri’un al’umma a rumfar zaben Bwari ta Abuja.
Asali: Legit.ng