Duk Wanda Ya Shiga Layi Kafin 2:30 Na Rana Zai Kada Kuri'a, Shugaban INEC

Duk Wanda Ya Shiga Layi Kafin 2:30 Na Rana Zai Kada Kuri'a, Shugaban INEC

  • Shugaban hukumar zabe INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, ya yi jawabi kan halin da ake ciki a zaben yau Asabar
  • Yakubu ya ce babu wanda INEC zata tauye wa hakkin jefa kuri'u matukar ya bi lokacin da doka ta tanada
  • An samu jinkirin bude wasu rumfunan zabe a sassan Najeriya kan dalilin da suka shafi tsaro da kuma kayan aiki

Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ce duk ɗan Najeriyan da ke kan Layi kafin karfe 2:30 na rana a rumfar zabensa zai kaɗa kuri'a.

Shugaban INEC na ƙasa, Farfesa Mahmud Yakubu, ne ya bayyana haka a wurin taron manema labarai ana tsaka da zaɓe a Abuja ranar Asabar. Ya ce ba wanda za'a tauye wa haƙƙi.

Farfesa Mahmud Yakubu
Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, yana jawabi. Hoto: INECNigeria
Asali: UGC

Farfesa Yakubu ya bayyana cewa na'urar tantance mai kaɗa kuri'a BVAS ta na aiki yadda ya kamata a dukkan sassan ƙasar nan, kamar yadda Channels ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan daba sun sace na'urar aikin zabe a jihar su Buhari da kuma wata jihar

A yau Asabar, 25 ga watan Fabrairu, yan Najeriya suka nufi rumfunan zaɓensu domin zaben wanda zai maye gurbin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A doka, za'a fara tantance mutane da kaɗa kuri'a daga karfe 8:30 na safe har zuwa karfe 2:30 na rana, amma kalilan daga cikin rumfunan zaɓe 176,606 ba su fara da wuri ba saboda wasu matsaloli.

Yayin da yake amsa tambaya kan jinkirin fara zabe, Farfesa Yakubu ya ce duk 'yan Najeriya masu katin PVC da suka hallara a rumfar zabe zasu kaɗa kuri'a.

The Nation ta rahoto Yakubu na cewa:

"Babu ɗan Najeriyan da zamu tauye wa haƙƙinsa. Eh tabbas mun bude wasu rumfunan a makare, mun yarda da haka a wasu wuraren amma tsarin da muka yi ya tanadi yadda za'a dawo da lokacin da aka rasa."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bayan Shugaban PDP, An Sake Samun Wani Shugaban Jam'iyya Ya Mutu a Abuja

"Ba mu na farawa karfe 8:30 na safe mu gama 2:30 na rana daidaita bane, ko da mun mun fara a makare bayan 8:30 ta gota, duk wanda ke kan layi sai ya jefa kuri'a duk tsawon lokacin da zai ɗauka."
"Saboda haka babu wanda za'a tauye wa hakkin zaɓe matukar yana kan layi a mazabarsa kafin karfe 2:30 na rana."

Shugaban Jam'iyyar Labour Party a Birnin Abuja Ya Kwanta Dama

A wani labarin kuma kun ji cewa shugaban Labour Party a mazabar Karshi, Abuja ya mutu a cikin bacci

Rahotanni sun nuna cewa an gama duk wasu shirye-shiryen zaben yau Asabar da shi jiya Jumu'a amma rai ya yi halinsa da daddare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262