Yanzu Yanzu: Shugaban Jam'iyyar PDP Na Abuja Ya Mutu a Ranar Zabe

Yanzu Yanzu: Shugaban Jam'iyyar PDP Na Abuja Ya Mutu a Ranar Zabe

  • Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, na Abuja, Sunday Zaka ya kwanta dama
  • Zaka ya mutu ne a ranar zabe sakamakon hatsarin mota a hanyarsa ta dawowa daga taron jam’iyya
  • Ya mutu tare da jami’in tsaronsa a tsakiyar garin Kuje da ke babban birnin tarayya

Abuja - Rahotanni da ke zuwa mana a yanzu shine cewa shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a babban birnin tarayya Abuja, Mista Sunday Zaka, ya mutu.

Mista Zaka ya mutu ne sakamakon wani hatsarin mota da ya cika da shi a Abuja a safiyar yau Asabar, 25 ga watan Fabrairu, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Tambarin gidan jaridar Legit Hausa
Yanzu Yanzu: Shugaban Jam'iyyar PDP Na Abuja Ya Mutu a Ranar Zabe
Asali: UGC

Marigayin ya mutu ne tare da jami'in tsaronsa bayan gudanar da wasu harkokin jam'iyyar a tsakiyar garin, rahoton Daily Post.

Ya mutu sakamakon hatsarin mota, Hadiminsa

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tashin Hankali Yayin Da Dan Majalisar PDP Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Wani Farmakin Neman Ransa

Wani hadimin marigayin, Bawa Benjamin, wanda ya tabbatar da faruwar al'amarin ta wayar tarho ya ce hatsarin ya faru ne da misalin karfe 2:00 na tsakar dare a hanyar Guda-Arena, a garin Kuje.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce motar marigayin kirar Peugeot ta kwace masa ne yayin da yake tuki sannan ta daki wani bishiya a hanyarsa ta zuwa gida bayan ya halarci taron sirri na jam'iyyar a Abuja.

Ya kuma bayyana cewa likitoci sun tabbatar da mutuwar marigayin bayan an gaggauta kai shi asitin koyarwa na jami'ar Abuja da ke Gwagwalada.

Shugaban karamar hukumar Kuje, Abdullahi Suleiman Sabo ma ya tabbatar da mutuwar shugaban na PDP.

Katsina: Yan sanda sunkama wasu mutum 15 kan zargin kokarin kutse a sakamakon zabe

A wani labarin, mun ji cewa rundunar yan sanda a jihar Katsina ta tabbatar da kama wasu mutane 15 bisa zarginsu da ake da kokarin kutse a sakamakon zaben da za a yi a ranar Asabar, 15 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An Shiga Zullumi A Jam'iyyar LP Yayin Da Dan Takarar Gwamna A Jihar Arewa Ya Yi Watsi Da Obi Ya Rungumi Tinubu

Kamar yadda kakakin rundunar, SP Gambo Isah ya bayyana, an damke mutanen ne dauke da kwamfiutocin laftof daban-daban da kuma manhaja mallakin wata jam'iyyar siyasa.

Isah ya ce tuni aka tsare wadanda ake zargin a sashin binciken laifuka domin gudanar da bincike kuma cewa za a sanar da jama'a sakamakon binciken da zaran an kammala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng