Babbar Magana Yayin Daka Nemi Tambarin Jam’iyyar Labour a Jikin Kuri’ar Zaben Ondo Aka Rasa
- An shiga tsaiko da tashin hankali yayin da jam'iyyar Labour ta gaza ganin tambarinta a takardun kuri'u na jihar Ondo
- Wannan lamari ya zo da tsaiko, mambobin jam'iyyar sun bukaci a dage zaben da za a yi a jihar a gobe Asabar
- Jam'iyyun siyasa da hukumar zabe gaba daya sun bayyana tsayawarsu da shiri a zaben 2023 kafin zuwan wannan tsaikon
Jihar Ondo - Jam'iyyar Labour ta shiga damuwa tare da yin magana bayan da aka nemi tambarinta aka rasa a jikin takardar kuri'a ta zaben gobe Asabar a jihar Ondo, Vaguard ta ruwaito.
Mambobin jam'iyyar Labour da yawa ne suka mamaye ofishin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ke Alagbaka don nuna adawarsu ga rashin jam'iyyarsu a kuri'un.
Takardun kuri'un, a cewar mambobin Labour na zaben da aka tsara yi ne na 'yan majalisun tarayya a gobe Asabar.
Mazabun da ba a ga tambarin Labour ba
Daily Trust ta tattaro cewa, ba a tambarin jam'iyyar Labour din ba a kuri'un mazabar sanata ta tsakiya a Ondo, Akoko ta Arewa masu Yamma/Arewa maso Gabas da Akoko ta Kudu maso Yamma/Kudu maso Gabas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakazalika, da na mazabar Akure ta Arewa/Kudu, Okitipupa/Irele, Ilaje/Ese-Odo da kuma Ondo ta Gabas/Yamma.
Ana son take hakkinmu ne
Daya daga cikin 'yan takarar jam'iyyar Labour ya zanta da jaridar, ina ya zargi INEC da cire jam'iyyar da gangan.
A cewarsa:
"Yanzu muka gano cewa takardun kuri'u da aka tura na zaben Sanata da 'yan majalisun tarayya a mazabar Ondo babu tambarin jam'iyyarmu (LP).
"Ina tunanin an shirya take hakkinmu ne a zaben gobe (Asabar). Wannan ba zai yiwu ba. Irin haka ya faru a Legas."
Da yawan mambobin jam'iyyar LP a jihar sun bukaci INEC da ta dage zaben da za a yi gobe a jihar.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun hukumar zabe mai zaman kanta ba.
Ana ci gaba da fuskatar matsaloli na siyasa a lokacin da zaben ke kara shigowa, an farmaki tawagar matar dan takarar PDP a Zamfara.
Asali: Legit.ng