A Karshe Kwankwaso Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Aka Kai Wa Magoya Bayansa Farmaki A Kano

A Karshe Kwankwaso Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Aka Kai Wa Magoya Bayansa Farmaki A Kano

  • Dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar NNPP ya bayyana yadda aka shirya hana shi shigowa Kano
  • Kwankwaso ya bayyana cewa an shirya kai hari kan magoya bayansa da nufin dakile shi daga shigowa Kano don cigaba da shirye-shiryen zabe
  • Kwankwaso ya tabbatar da cewa za a samu chanji idan Allah ya sa ya zama shugaban kasa a zaben shugaban kasa na 25 ga watan Fabrairu

Jihar Kano - Rabiu Kwankwaso, dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar NNPP, ya ce an farmaki magoya bayan sa lokacin da ya ke gangamin yakin neman zabe a Na'ibawa-Titin Zaria a Kano.

Kwankwaso yayi jawabi yayin da ya ke tattaunawa da yan jarida dangane da abin da ya shafi zabe da Sha'anin tsaro a Kano ranar Alhamis, rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Zabe Ya Gabato, Har Yanzu Babban Ministan Buhari Ya Ki Yarda Ya Goyi Bayan Tinubu

Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso dan takarar shugaban kasa na NNPP da abokin takararsa wurin kamfe. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An so hana ni shigo wa birnin Kano ne - Kwankwaso

Ya ce harin da aka kai wa magoya bayansa shiri ne na hana shi shigowa birni.

Tsohon gwamnan na Kano ya bayyana gamsuwarsa da kammala yakin neman zabensa cikin nasara a kananan hukumomin kasar nan sama da 500.

Kwankwaso ya ce bai samu ko da alamun rashin nuna goyon baya gare shi ba daga wajen mutane a lokacin da yake yawon neman kuri'a yana mai cewa ko tsakuwa ba wanda ya jefi shi da ita.

Ya ce:

''Da farko, ina so na fara godewa Allah da masoya na a fadin Kano da Najeriya, musamman yankunan da na ziyarta. Ina tunanin a tarihin Najeriya, ni kadai ne dan takarar da na zagaya kowacce jiha, mun yi zagaye a wurare da dama amma kafin muje kan wannan, ina son godewa yan Najeriya bisa goyon bayansu, muna samun goyon baya mai tarin yawa tun lokacin da muka bude wannan jam'iyyar''

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Kutsa Cikin Gidan, Sun Harbe Shugaban Jam'iyya Har Lahira

''Da yardar Allah, mun yi yakin neman zabe ko ina a fadin jihohi da garuruwa kuma yau jam'iyyar mu ta sanu kamar sauran jam'iyyu."
"Ina cikin farin ciki, tun da muka fara yakin neman zabe, yau na zagaya kananan hukumomi kusan 500 daga cikin 774 da mu ke da su.
''Babban abin farin ciki shine tun bayan kafa jam'iyyar mu, da farko mun bude ofisoshi, muka fara yakin neman zabe, mun ziyarci wurare da dama, muna gabatar da jam'iyyar tare da gabatar da kudirin ciyar da kasar nan gaba idan mun yi nasara a zabe."
''Yau ina cikin farin ciki, zanyi bacci ina murna ta wani bangaren, ta wani bangaren kuma ina bakin ciki. Mun zagaya Najeriya, munje kudu da gabas ba tare da mun samu matsala ba har sai lokacin da zamu zo kano. Jiya da daddare wani daga gidan gwamnati ya kira ni ya ke fada min suna tattaunawa kan yadda za a hana ni shigowa Kano ta kowanne hali."

Kara karanta wannan

Kamfen din karshe: 'Yan daba sun farmaki magoya bayan Kwankwaso, sun kone motoci a Kano

Ya cigaba da jawabi kamar haka:

''Ba yakin neman zabe zan zo Kano ba, na gama komai tun a Kaduna. Na kawo ziyara kano ne kawai don shirye-shiryen zabe, saboda nima in fita in kada kuri'a ranar zabe amma bayanan da na samu shine gwamna da daraktan hukumar SSS sun shirya yadda za su kawo mana hari.
''Mutane na ta cewa mu chanja hanya amma na fada musu cewa magautan mu za su iya samun bayanai. In da chanja hanya zai tseratar da magoya baya daga harin da na chanja.
''Ko a lokacin zaben 2015 da 2019, haka akayi ta shirya min amma ba saboda su ne bana zuwa. A duk Najeriya, ba wanda zai iya fitowa ya ce yana bin Rabiu Kwankwaso naira daya, ko lokacin da na ke gwamna ba wanda ke bina bashi.
''Jam'iyya sun rubuta mu su takarda cewa za mu zo kuma sai muka samu labari ana shirya taro a gidan gwamnati don kawo mana hari da lalata mana motoci.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Zai Dura Kano Domin Yin Yawon Kamfen Karshe a Yakin Zaben 2023

''Abin mamaki, so su ke su hana ni, Rabiu Musa Kwankwaso, dan takara kuma dan asalin jihar Kano da ya ke da yancin shiga Kano a tsari na dimukradiyya. Ba taro muka zo yi ba, ko magoya baya na suna son yin taro, me yasa za a hana?
''Yau, ni ba kansila ba, sanata, ko gwamna, bani da aikin komai a kasar nan. Neman aiki ma nake, a yanzu. Ni na ke neman yan Najeriya su bani aiki. Da yardar Allah, yan Najeriya za su ga chanji in na ci zabe.''

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164