Yadda Tururuwar Mutane Sukayi Farin Dango A Kano Domin Tarbar Kwankwaso

Yadda Tururuwar Mutane Sukayi Farin Dango A Kano Domin Tarbar Kwankwaso

  • Ɗan Takarar na Shugaban Ƙasar na Jam'iyyar NNPP, Kwankwaso ya Isa Kano ne a Wani Salo Tamkar Ya Shekara Ɗari Ba'a Gansa ba
  • Tafiyar Tasa ta Hadu da Matsala Daga Wasu Yan Jagaliyar Siyasa Hartakai ga Kone Motoci Tare da Jin Ciwo
  • Gwamantin Kano Ta Nesanta Kanta da Wadanda Aka Kama Sunje Wajen Kai Hare-Hare Ta Bakin Kwamishinan ta

Yayin da ake sa rai gobe za'a kaɗa ƙuriar zaɓen shugaban ƙasa dana ƴan majalisu, yan takarkari daga ko wanne ɓangaren na siyasa na komawa mahaifar su

Suna komawa ne cikin mazaɓun su dake cikin jihohin su domin yin zaɓen tare da tabbatar da sun kawo mazaɓun su wanda hakan zai bawa Kowa damar nuna cewa ko a gida shima sarki ne.

Injiniya Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso shima ba'a barsa a baya, domin kuwa a jiya shima ya isa Garin Kano da daddare domin gabatar da yakin neman neman zaɓen sa, sannan kuma ya tsaya domin kada ƙuriar sa.

Kara karanta wannan

An Garƙame Iyakokin Najeriya Domin Gudanar da Babban Zaɓen Ƙasa.

Kwankwasiyyaaman
Yadda Tururuwar Mutane Sukayi Farin Dango A Kano Domin Tarbar Kwankwaso Hoto: Newsdigest
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da ake sa rai gobe za'a kaɗa ƙuriar zaɓen shugaban ƙasa dana ƴan majalisu, yan takarkari daga ko wanne ɓangaren na siyasa na komawa mahaifar su

Tunda fari dai, zuwan na ɗan takarar jam'iyyar ta NNPP ya ƙunshi abubuwa masu ban mamaki da al'ajabi.

Abun da ya ɗauki hankali baya rasa nasaba da yadda aka ga cincirindon masoya daga tsagin matasa, sanye da jajayen huluna da hijabai dake nuna tambarin kwankwasiyya.

Tun da safiyar Alhamis aka ga ɗaruruwan matasan daga tsagin maza da mata nata jerin gwano zuwa Kwanar ɗan gora domin amsar ɗan su, kuma jagoransu.

Kwankwaso ya samu isowa Kwanar Ɗangora ne tun da rana tsaka daga garin Kaduna amma saboda cincirindon jama'a da sukayi kama da farin ɗango, ɗan takarar shugabancin ƙasar bai samu isa gidan sa dake Miller Road ba sai wajen 8:25 na yamma.

Kara karanta wannan

Hasashen Zaɓen 2023: Jerin Jihohin Da Kowanne Daga Cikin Manyan Ƴan Takara 4 Zai Lashe Babu Tantama

Wannan tafiya ce da bata wuce kayi ta a cikin awa ɗaya bane idan babu wani abu irin haka.

Tafiya ce mai cike da ƙalubale, domin hattana Jaridar Daily Trust sai da rawaito yadda aka farwa mabiya bayan Kwankwaso da hari tare da ƙona musu motoci daga wasu mutane ɓata gari da ba'a gama tantance su ba.

Harin dai ya faru ne akan titin Zariya, duk da cewar jami'an tsaro sun yi ƙoƙari sosai wajen dawo da doka da oda.

Mai magana da yawun jam'iyyar NNPP Sanusi Bature ya shaidawa majiyar mu cewar, yadda mutane suke zato ba haka bane.

A cewar sa, Kwankwaso bai zo don yaƙin neman zaɓe ba, hasali ma yazo gida ne kawai, kuma taro da shauƙin jama'a ne yasa suka fito haka. Domin jama'ar ta taru ne kawai domin karɓar sa tare dayi masa maraba.

Hakan ya fito ne a wani saƙo daya fitar jim kaɗan da iso war madugun na kwankwasiyya.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Mumunan Hari Ofishin Yan Sanda, Sun Banka Mata Wuta

Inda yace, Kwankwaso na tare da Abba K. Yusuf, da mataimakin sa Kwamaret Aminu Abdussalam Gwarzo da sauran ƴan takarkarun jam'iyyar Sanatoci na jam'iyyar NNPP ta Kano.

Bature ya ƙara da cewa:

"Mun samu nasarar hamɓarar da wani tuggun da jam'iyyar APC mai mulkin Kano ta assasa na hana magoya bayan mu damar da kundin tsarin mulkin Najeriya ya bamu na yin taron siyasa.
" Muna yabawa da haɗakar jami'an tsaro na ƴan sanda da sojoji, domin sun kama kimanin mutane 300 na daga ƴan jagaliyar siyasa da aka turo su kaso mana hari akan rayukan mu da abin hawar mu." Inji Shi.

To sai da kuma mataimakin kakakin kamfen na APC wanda shine kwamishinan ruwa na jihar Kano, Garba Yusuf, tuni ya ƙi yarda da batun, inda ya ƙaryata ta, tare da faɗin ba komai bane face shafcin gizo da ƙoƙi.

Kwamishinan yace babu yadda za'ai su kasance masu turo ƴan jagaliyar siyasa su aikata ta'addanci akan mutanen Kano

Kara karanta wannan

Saura Kwana Biyu Zaɓe, Tinubu Yayi Wani Babban Kamu A Abuja

A cewar kwamishinan:

"Babu saka hannun mu ko kaɗan, mu munjanye daga yaƙin neman zaɓen mu saboda shawarar da ƴan sanda suka baiwa duk wata jam'iyya dake Kano aka. kada suyi taro jiya. Saboda haka, APC, da gwamnatin Kano, basu da masaniya a cikin wannan balahirar," inji shi.

Al'amuran zabe dai nata ƙara kankama yayin da ake da ƙasa da awanni 24 domin gudanar da babban zaɓe na ƙasa.

Abin jira dai a ganmi shine yadda zata karke a zaben da zai wakana a gobe Asabar 24/02/2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida