Kano: DSS Ta Gano Bindigu, Takubba Da Sauran Muggan Makamai A Ofishin Kamfen

Kano: DSS Ta Gano Bindigu, Takubba Da Sauran Muggan Makamai A Ofishin Kamfen

  • Hukumar yan sandan farin kaya DSS ta ce ta gano wasu muggan makamai a wani gida da ke kan hanyar Airport Road a Kano
  • Kakakin DSS, Peter Afunanya, ya tabbatar da hakan cikin wata jawabi da ya fitar, yana mai cewa sun gano bindigu, takubba, wukake ds
  • Afunanya ya kuma karyata cewa hukumar ta DSS tana tsorata wata jam'iyyar siyasa a Kano yana mai cewa hukumar ba ruwanta da zaben bangare

Jihar Kano - Yan sandan farin kaya a ranar Juma'a ta ce ta gano wasu makamai daga wani gida da ke kan titin Airport Road, karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano, rahoton The Punch.

Hukumar ta karyata zargin da wata jam'iyya ta yi na cewa tana tsoratar da mambobinta.

Taswirar Kano
Taswirar Jihar Kano. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Duk da cewa kakakin na DSS, Peter Afunanya, yayin bayyana cewa sun shirya wa zaben bai ambaci sunan jam'iyyan ba, binciken da Punch ta yi ya nuna cewa jam'iyyar NNPP reshen jihar Kano ta zargi hukumar da tsorata mambobinta da kai samame ofishinsu na kamfe.

Kara karanta wannan

Zaben jibi: Rudunar soja ta fitar da sako mai daukar hankali ga dukkan 'yan Najeriya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Afunanya ya ce ana aiki domin gano yadda makaman suka isa gidan da aka gano su.

Wani sashi na sanarwar ya ce:

"Domin samar da yanayi mai kyau don zabe, hukumar ta dauki matakan rigakafi da tattara bayanan sirri a jihar. Misali a ranar 22 ga watan Fabrairun 2023, hukumar bisa ka'ida ta bincika wani gida da ke Airport Road, karamar hukumar Nasarawa, Jihar Kano.
"Yayin binciken, ta gano muggan makamai har da bindiga, wuka, takubba, da sauransu a ginin.
"Don haka zargin cewa ana tsorata wata jam'iyya daya a jihar ba gaskiya bane; idan ko haka ne ta yaya aka gano makaman a wurin? Shin na rikicin zabe ne? Ko a Kano ko wani wuri, hukumar tana bawa dukkanin jam'iyyu dama guda na yin halastattun harkokinsu. Za mu iya fadan hakan ba tare da shakka ba."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar NNPP a Kano Tace Jami'an Na Kai Musu Hare-Hare Ofishin Kamfe

Yan siyasa ne neman bata sunan Yusuf Bichi, in ji DSS

A wani rahoton kun ji cewa hukumar yan sandan farin kaya, DSS, ta ce wasu gurbatattun yan siyasa na kulla makirci domin bata sunan shugabanta na kasa, Yusuf Bichi, da wasu manyan ma'aikata.

Mr Peter Afunanya, mai magana da yawun hukumar ne ya bayyana hakan yana mai cewa wasu yan siyasa a cikin gwamnati da wajenta na kokarin kawo tangarda ga ayyukan hukumar na hana barna a kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164