Wata Sabuwa: Ƴan Bindiga Ɗauke da Muggan Makamai Sun Kaddamar da Hari Mai Muni wa Ofishin Yan Sanda a Abia

Wata Sabuwa: Ƴan Bindiga Ɗauke da Muggan Makamai Sun Kaddamar da Hari Mai Muni wa Ofishin Yan Sanda a Abia

  • Yan Bindigan Sun Dira a Ofishin Dauke da Muggan Makamai tare da Harbin Kan Mai Uwa da Wabi a Wajen
  • Har ila Yau, Sun Farmaki Ofishin DPO din Yan Sandan, Tare da Hargitsa Komai na ciki, Duk da Zakara ya Bashi Sa'a
  • Sun Kone Komai na Ofishin tare da Jikkata Wani Kwanstabulari ta Hanyar Kwaftara Masa Gatari a Goshi

Abia - A yau Alhamis ne wasu ƴan bindiga da za'a iya kira da ƴan bindiga-daɗi suka ƙaddamar da wani mummunan hari a wani ofishin ƴan sanda dake yankin Ugwunagbo ta jihar Abia.

Lamarin na zuwa ne, ƙasa da awanni arba'in da takwas domin gudanar da zaɓukan ƙasar.

An ruwaito cewar, lamarin ya faru ne a yayin da wasu yan sanda guda biyu suke tsaka da aikin su, kafin daga bisani maharan suzo musu da wani salo irin samfurin kwantan ɓauna.

Kara karanta wannan

Yan Boko Haram Yunwa Da Hare-Hare Yasa Sun Koma Sace Mutane Tare Da Neman Kudin Fansa

Zuwan su keda wuya, sai suka soma aman wuta kota ina batare da ƙaƙƙautawa ba. Hakan yasa ƴan bindigan suka fi ƙarfin yandan guda biyu, wanda saboda haka ne suka cinnawa ofishin wuta nan take.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Police station
Ire iren Ofishisoshin Yan sanda da ake konawa a Abia Hoto: Punchng.com
Asali: UGC

Babban ɗan sandan yankin da aka fi sani da DPO ya tsallake rijiya da baya, domin rahoton da Jaridar The Nation ta saki, ya nuna DPO ɗin aka so a kashe.

To amma sai yayi sa'a, lokacin da aka kawo harin baya ofishin, saboda rabon ganin baɗi.

Ana kyautata zaton maharan sun saki ɗaurarru tare da yin awon gaba da makamai na ƴan sanda dake ajiye.

Majiyar shaidu ta ido da ido ta faɗi cewa, masu harin sunyi ƙoƙarin gano wajen ne domin yanayin wajen kamar baida isasshen ƙarfi da zai iya kawo wa shirin nasu tasgaro.

Kara karanta wannan

Yan Watanni Bayan Rabuwa Da Matarsa Da Kuma Musulunta, JJC Skillz Yayi Aure A Kano

Jawabin hukumar yan sanda

Geoffrey Ogbonna, shine mai magana da yawun hukumar ƴan sanda ta jihar Abia, ya tabbatar da faruwar lamarin lokacin da yake cewa:

"Da misalin ƙarfe 3 na dare, wasu marasa tarbiyya kimanin su talatin sun afkawa ofishin mu yanki dake Ugwunagbo ta gundumar Ihie wanda har suka yi musayar wuta da mutanen mu dake kan gaɓaren aiki. Hakan ya basu damar shiga sannan suka cinnawa ofishin wuta."

Mai magana da yawun yan sandan ya tabbatar da cewa, ɗan sanda ɗaya ya samu rauni , kuma tuni aka garzaya dashi asibiti inda yanzu yake amsar maganin a wani yanayi na ujila.

Ya kuma tabbatar wa manema labari cewa, hattana ofishin shugaban ƴan sandan dake wajen basu ƙyale, domin sun kacaccala komai.

A kalaman sa:

"Sun cinnawa motocin suntiri guda biyu wuta, baya ga ofishi tare da samfewa da makamai da muka ajiye a motar sulken mu, sannan sun bugawa wani kwanstibulari adda a goshi."

Kara karanta wannan

Zaɓukan 2023: Tinubu ya Aikawa Atiku da Obi Ƙwaƙwƙwaran Saƙo Bayan INEC Ta Ayyana Shi a Matsayin Mai Nasara

Daga ƙarshe Geoffrey Ogbonna yayi Allah wadai da lamarin, tare da tabbatar da cewa bincike yana nan yana gudana abisa umarnin kwamishinan ƴan sandan jihar domin gano maharan.

Inda ya roƙi jama'a, dasu bada bayanai na duk wani abu da zai taimaka zuwa ga kama maharan.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida