Sauya Takardar Naira: Buhari Bai Saba Umurin Kotun Koli Ba, In Ji AGF Malami

Sauya Takardar Naira: Buhari Bai Saba Umurin Kotun Koli Ba, In Ji AGF Malami

  • Antoni Janar na tarayya kuma ministan shari'a, Abubakar Malami, ua ce gwamnatin tarayya ba ta saba umurnin kotun koli kan sauya naira ba
  • Malami ya yi wannan maganan ne yayin jawabin da ya yi wurin taron ministoci da tawagar sadarwa ta shugaban kasa ta shirya
  • Shugaba Buhari, a jawabin da ya yi wa kasa a ranar Alhamis, ya umurci CBN ta mayar wa al'umma tsaffin N200, amma tsaffin N500 da N1000 sun haramta wanda ya saba umurnin kotun koli

Abuja - Antoni Janar na kasa kuma ministan shari'a Abubakar Malami a ranar Alhamis ya ce Shugaba Muhammadu Buhari bai saba umurnin kotun koli ba kan batun wa'adin dena amfani da tsaffin kudi da wasu gwamnonin jihohi suka yi kararsa.

AGF din ya ce idan dai doka ake magana, akwai zabi daban-daban, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zafafan Hotunan Kamfen Tinubu/Shettima Na Karshe Da Ya Gudana a Legas

Abubakar Malami
Abubakar Malami ya ce FG ba ta saba umurnin kotin koli ba kan wa'adin dena amfani da tsaffin naira. Hoto: The Cable
Source: Facebook

Malami ya yi wannan jawabin ne a wurin taron ministoci karo na 67 da aka yi a gidan gwamnati a ranar Alhamis, The Nation ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A ranar 8 ga watan Fabrairu ne kotun kolin ta bada umurni na hana babban bankin kasa, CBN, bada wa'adin dena amfani da tsaffin N200, N500 da N1000.

Kotun ta bada umurnin ne biyo bayan karar da gwamnonin jihohin arewa guda uku - Kogi, Kaduna da Zamfara suka shigar.

Duk da umurnin kotun, Shugaban kasar a jawabin da ya yi a ranar 16 ga watan Fabrairu, ya ce ya umurci CBN ya raba wa al'umma tsohon N200, ya kuma ayyana tsaffin N500 da N1000 a matsayin haramtattun kudi.

Abin da ke faruwa a baya-bayan nan game da tsarin sauya naira, Abubakar Malami, CBN, zaben 2023

Kara karanta wannan

Adamu da Gwamnoni 4 Sun Gana da Ministan Buhari Kan Sauya Naira, Sabbin Bayanai Sun Fito

Umurnin na shugaban kasa ya saba abin da kotun koli furta na cewa a cigaba da amfani da tsaffin takardun nairan har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan karar da gwamnonin jihohi suka shigar.

Jawabin na shugaban kasa ya janyo suka daga wasu yan Najeriya da ke ganin shugaban kasar ya saba umurnin kotun koli.

Wani sashi na jawabin Malami ya ce:

"Gaskiyar ita ce, karara, ba mu saba wa duk wani umarni da kotu ta bayar ba, har da duk wani umarni da ya shafi sake fasalin naira. Ba mu saba doka ba. Na yi imanin ni ba ma'aikacin banki ba ne amma ba ku je ku gano bankin da kuka je ba don gabatar da takardun N1000 ko N500 da aka ki karba. Don haka ba mu keta doka ba."

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164