Jam'iyyar PDP Ta Rushe Tsari, Ta Koma Inuwar APC a Karamar Hukumar Jihar Borno

Jam'iyyar PDP Ta Rushe Tsari, Ta Koma Inuwar APC a Karamar Hukumar Jihar Borno

  • Saura awanni 48 zaben shugaban ƙasa, jam'iyyar APC ta ƙara karfi a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya
  • Jam'iyyar PDP baki ɗayanta a karamar hukumar Magumeri ta nutse cikin APC domin goyon bayan gwamna Zulum
  • A cewar jagoran masu sauya shekar sun ɗauki matakin ne domin nagartar shugabancin Zulum

Borno - Jam'iyyar PDP a ƙaramar hukumar Magumeri, jihar Borno ta nutse cikin inuwar jam'iyyar APC domin goyon bayan ta zarcen gwamna Babagana Zulum da sauran 'yan takarar jam'iya mai mulki.

Leadership ta tattaro cewa Magumeri na can a arewacin jihar Borno kuma nan ne mahaifar shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Zanna Gaddama.

Jam'iyyar APC.
APC ta kwamushe baki ɗaya PDP a karamar hukumar Magumeri. Hoto: leadership
Asali: UGC

Dubbannin masu sauya shekar sun samu kyakkyawar tarba daga gwamna Zulum wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Umar Usman Kadafur, ranar Talata a garin Magumeri.

Kara karanta wannan

"Ku Fito Kwanku Da Kwarkwatanku Ku Zabi Atiku a Ranar Asabar" - Jiga-Jigan PDP Ga Al'ummar Lagas

'Yan siyasan sun koma APC ne ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban PDP na Magumeri, Modu Fuwumi, da ɗan takarar majalisar dokokin jiha a zaben ranar 11 ga watan Maris.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ɗaruruwan masu sauya shekar sun kunshi shugabannin PDP na gundumomi, shugabannin matasa da sauran jagororin jam'iyyar a dukkan gundumomin Magumeri.

Meyasa suka koma APC?

Shugaban PDP na Magumeri kafin wannan lokaci, Honorabul Fawumi, ya ayyana cewa daga komawarsu APC, babu sauran PDP a ƙaramar hukumar, ta mutu murus.

Da yake bayanin dalilin da yasa suka nutse baki ɗaya tsarin PDP zuwa APC a yankin, tsohon shugaban ya ce sun yi haka ne saboda nagartar shugabancin Zulum a shekaru uku da rabi da suka wuce.

Ya ce Borno ta samu shugabancin da babu kamarsa wanda ya jawo ci gaba mara adadi a sassan garuruwan kananan hukumomi 27 da ke faɗin jihar.

Kara karanta wannan

Ana Gab Da Zabe, Atiku Ya Kara Karfi a Arewa, Dan Majalisa Mai Ci Da Hadimin Gwamna Sun Fice Daga APC Zuwa PDP

Bugu da ƙari, ya yaba wa shugaban ƙaramar hukumar Magumeri, Dakta Yaumi Ali, bisa dumbin nasarori da ci gaban da ya samar a yankin, kamar yadda jaridar Independent ta rahoto.

Kafin wannan sauya sheƙa, kusan 'yan takarar majalisar dokoki Bakwai daga PDP da SDP suka koma APC cikin wata ɗaya wanda ya nuna aminta da jagorancin Zulum ta ko ina.

Rigingimin PDP sun bude sabon shafi

A wani labarin kuma Ana dab da zabe ranar Asabar Jam'iyyar PDP Ta Kori Dan Takarar Gwamna a Jihar Akwa Ibom

Jam'iyya mai mulkin jihar Akwa Ibom ta tabbatar da korar ɗan takarar gwamna, a zaben 11 ga watan Maris, 2023, Michael Enyong.

Jam'iyyar ta bayyana cewa ta ɗauki mataki kan ɗan takarar ne saboda tuhumar da ake masa ta amfani da takardun bogi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262