‘Fidelity’: Maroki Ya Buga Roko, Attajira Ta Nemi Ya Ba da Lambar Asusu, Martaninsa Ya Ba da Nishadi
- Bidiyon wani maroki ya jawo cece-kuce da nishadi a kafar sada zumunta ganin yadda ya zo da sabon salo
- Ganin cewa babu tsabar kudi a hannun jama’a a kasar, marokin ya nemi a tura masa kudi asusunsa na banki
- An ji mutumin na ambatan sunan wani banki daga cikin fitattun bankunan kasar nan, ya fadi lambar akant
Maroki ya kada gurmi ga wata mata a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar karancin tsabar kudi, ya ba da mamaki.
A wani bidiyon da ya yadu a kafar sada zumunta ta Instagram, an ga marokin tare da dan amshinsa suna rera wakar yabo ga wata mata.
Matar da suke kada wa roko na zaune a cikin mota, sai ta tambaye su lambar asusun banki sai kawai ya fara fadi a cikin wakar.
Bayan fadin lambar asusu, sai aka tambaye shi sunan banki, shi kuwa ya amsa da ‘peedility’, ma’ana bankin Fidelity.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalli bidiyon:
Martanin jama’a
Jama'ar kafar Instagram sun ce ba za a yi babu su ba, sun nishadantu da wannan kidi, sun yi martani mai daukar hankali. Ga kadan daga ciki:
jesichun:
"Ina kaunar kasar nan!!!"
temi_are39:
"Wannan mutumin ya nishadantar dani...bari na tura masa wani abu fiifiliti.”
isimemematt:
"Bari naje na turawa wadannan mutanen wani abu. Ya min dadi.”
radcheval:
"A bar batun a gefe, wannan Yarbanci ne da tsarmin Arewa? Ban san ‘yan Arewa na amfani da ganga irin wannan ba su ma.”
lammylinky:
"....matukar baka karbar tiransfa a wannan yanayin da kasar ke ciki ka yi kuskure.”
yackzofficial:
"Peediliti"
onyeubanatu1:
"Baba ka duba FeeDeeLeeTee dinka.”
adamzandevez:
"Kai dole na tura wani abu domin na nishadantu.”
mg_pixels_:
"Zan tura masa kudi yanzu-yanzu.”
janetheconsulgeneral:
"Pidility kalli nishadin ‘cashless’.”
itscampbell.e:
"Wannan ci gaba ne mai kyau. Ni fa na jima bana rike tsabar kudi tun 2020. Mahajojin biyan kudi sun mamaye komai. Naija na bukatar ta girma.”
A halin da ake ciki, 'yan Najeriya na ci gaba da fuskantar tashin hankalin karancin sabbin Naira, hakan na shafar kasuwanci da harkokin yau da kullum a bangarori daban-daban na kasar, musamman yayin da aka kusa zabe.
Asali: Legit.ng