Karancin Naira: Kwastomomi Sun Banka wa ATM Wuta a Jihar Legas
- Daga karewar kudi, wasu fusatattun kwastomomi sun cinna wa na'urar cire kuɗi a banki ATM wuta a jihar Legas
- Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya ce tuni dakarun yan sanda suka shawo kan lamarin
- Tun bayan sauya fasalin naira, yan Najeriya sun tsinci kansu cikin wahala saboda rashin wadatar sabbin kuɗi
Lagos - Wasu fusatattun kwastomomi sun bankawa na'urar ATM wuta a wani banki da ba'a bayyana ba a yankin Idi Araba, jihar Legas bayan kuɗin da ke ciki sun ƙare.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa lamarin dai ya kawo tsaiko a harkokin bankin domin sai da ta kai ga aka tura jami'an yan sanda kai ɗauki.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce zaman lafiya ya dawo a yankin.
Sai dai mai magana da yawun yan sandan bai bayyana sunan bankin da lamarin ya shafa ba, haka zalika bai ce komai ba game da kama waɗanda suka aikata ɗanyen aikin ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Da safiyar nan a yankin Idiaraba, kuɗi suka kare a ATM mutane suka fusata suka banka masa wuta. Nan take jami'ai daga Caji Ofis mafi kusa suka kai ɗauki wurin."
"Tuni aka kashe wutar kuma an shawo kan mutanen da ke wurin kuma tun lokacin harkokin bankin ya ci gaba kamar yanda aka saba."
- Benjamin Hundeyin.
Tribune Online ta tattaro cewa zanga-zanga ta ɓarke da sassan Najeriya a 'yan kwanakin nan sakamakon wahalhalu da karancin naira.
Da yawan 'yan Najeriya sun wayi gari cikin yanayin damuwa bayan babban bankin Najeriya ya sauya fasalin N200, N500 da N1000 kuma sabbin basu wadata ba.
Fusatattun kwastomomi sun ƙone Bankuna da yawa a bangarori daban-daban na ƙasar nan saboda rashin samun damar cire kuɗi daga asusun bankunansu.
CBN Ya Fara Rabawa Mutane Takardun Sabon Naira Gida-Gida a Kano
A wani labarin kuma CBN ya bullo da sabon tsarin da zai warware wa Kanawa matsalolinsu game da karancin naira
Babban bankin ya aika wakilai zuwa kananan hukumomi uku a Kano domin su bi gida-gida suna musanyawa mutane sabbin takardun naira.
Asali: Legit.ng