Kotu Ta Amincewa Gwamnati Kwace Wasu Kadarorin Gwamnan Kogi Guda 14

Kotu Ta Amincewa Gwamnati Kwace Wasu Kadarorin Gwamnan Kogi Guda 14

  • Gwamnatin tarayya ta samu nasarar mallaka na wucin gadi na wasu kadrori guda goma sha hudu
  • Wadannan dukiyoyi suna birnin tarayya Abuja, jihar Legas a kudu da kuma hadaddiyar daular Larabawa
  • Ana zargin cewa wadannan dukiyoyi mallakin gwamnan jihar Kogi ne, Alhaji Yahaya Bello Adoza

Legas - Babban kotun tarayya dake zamanta a jihar Legas a ranar Laraba ya bada umurnin gwamnati ta mallake dukiyoyi 14 dake Abuja, Legas da kasar UAE da ake zargin na gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ne.

Kotun tace gwamnati za ta iya mallake kadarorin kafin kammala shari'ar, rahoton Leadership.

Hakazalika Alkalin kotun, Nicholas Owiebo, ya bada umurnin kwace kudi N400million da ake zargin na gwamnatin jihar Kogi ne daga hannun wani Aminu Falala.

Ya bada wannan umurni ne bayan karar da hukumar yaki da almundahana EFCC tayi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Jihar Rivers Ya Shiga Karar Gwamnoni Da Buhari Kan Naira A Kotun Koli

Yahaya Bello
Gwamnan Kogi Da Ake Zargin Mallakinsa ne Gidajen Guda 14
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Lauyan EFCC, Rotitmi Oyedepo, ya bayyana cewa dukiyoyin sun hada da wani dake Bujr Khalifa a Dubai, UAE inda ake zargin da kudin haram aka saya.

Oyedepo ya sanar da kotu cewa an gano kudi N400million an sameshi ne ta hanyar haram kuma nan niyyar sayan fili mai lambar Plot No. 1224 Bishop Oluwole Street, Victoria Island, Lagos.

Alkalin ya umurni hukumar EFCC ta wallafa wadannan kadarori a jaridu nan da makonni biyu saboda idan akwai wanda zai iya fitowa yace nasa ne, ya fito.

Shari'ar kotun koli game da lamarin Naira, Gwamna Wike ya shiga

A wani labarin kuwa, Gwamnatin jihar Rivers ta shiga karar da gwamnatocin jiha goma (10) suka shigar kan gwamnatin tarayya game da lamarin sauya fasalin Naira.

Karar da gwamnatin jihar Kaduna, Kogi, da Zamfara suka fara shigarwa a makonnin baya na kira ga kotun koli ta dakatar da gwamnatin tarayya wajen tilasta daina amfani da tsaffin takardun kudi N200, N500 da N1000.

Kara karanta wannan

Gwamna Ganduje Yace China Ta Kawo COVID-19, CBN Ya Kawo COVID-23

A ranar 8 ga Febrairu kotun koli ta dakatar da CBN daga hana amfani da tsaffin Naira kafin ta yanke hukunci kan lamarin.

Tun daga lokacin sauran jihohi bakwai suka shiga lamarin suna masu goyon bayan takwarorinsu.

Kotun yanzu ta dage zaman zuwa ranar 3 ga wayan Febrairu, 2023 don yanke hukuncin karshe wannan lamari da yaki ci, yaki cinyewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida