“Zuciyata”: Matashi Ya Yi Shiga Kamar Mahaukaci Yayin da Yake Nuna Kauna Ga Mahaukaci a Bidiyo
- Wani mutum ya baiwa mutane da dama mamaki da irin karamcin da ya nunawa wata mata mai lalurar tabin hankali
- Mutumin ya yi shiga irin ta mahaukata sannan ya zanta da matar mai tabin hankali wacce ke gudanar da harkokin gabanta
- Matashin mai tsananin kirki ya dungi binta a baya sannan ya bata ruwa domin ta jika makoshi daga robar ruwansa
Bidiyon wani dan Najeriya da ke nunawa wata mata mai lalurar tabin hankali kauna a titi ya haifar da cece-kuce a soshiyal midiya.
Mutumin da aka fi sani da mahaukacin TikTok ya dungi bin matar mai tabin hankali a baya bayan ya ganta tana wucewa yayin da shi kuma yake daukar bidiyo.
Mutumin wanda ke sanye da tsummokara ya karfafawa kansa gwiwa sannan ya kira ta, amma sai mahaukaciyar ta share shi.
Ya matsa kusa da ita sannan a hankali ya mika mata ruwa daga goran robar da ke hannunsa bayan ya sha.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Bayan nan kuma, sai ya bata biredi sannan ya taimaka wajen hada mata sauran da ragowar ruwan.
Cike da zolaya, mutumin ya so ya kara shan ruwan bayan ya bata ta sha amma sai ya sauya tunani.
Bidiyon wanda ya yadu a manhajar TikTok ya haddasa cece-kuce.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
omodaratan feyisayo ta ce:
"Wannan shine ainahin misalin kafin ka kama biri sai kaima ka zama daya."
Taiwo ya ce:
"Menene dalilin da yasa ka dauki sanda a hannu, saboda kare kai ko koda idan ta so gantsara maka cizo."
excelbae1 ya ce:
"Ka tabbata kai dinma ba mahaukaci bane amma kana da karfin hali fa mutumina kana da karfin hali."
STEFAN ♋ ya ce:
"Wannan ita ce soyayya ta gaskiya❤️so na hakika."
Leo Nwanze ya ce:
"Ina ta tsammanin za ka sake shan ruwan bayan ka bata, ka karya mun zuciyata."
Bidiyon uwa mai hannu daya tana tsantsarawa diyarta kitso ya ja hankali
A wani labari na daban, wata mata mai hannu daya ta burge jama'a da dama tare da basu mamaki bayan ganin bidiyonta tana nunawa diyarta kauna.
Duk da kasancewarta mai hannu daya, tana amfani da shi a haka wajen tsantsarawa diyarta kitso mai kyau.
Asali: Legit.ng