"Tinubu Bai Bani Ko Sisi Ba": Jarumar Fina-Finan Najeriya Ta Yi Martani Ga Masu Sukar Ta
- Jarumar masana'antar Nollywood ta yi martani akan masu zagin ta saboda goya wa Tinubu baya
- Jarumar Toyin Abraham, ta ce ba abin da tsinuwar da zagin za suyi mata saboda bata karbi kudin kowa ba
- Ta kara da cewa ita ma yar kasa ce kamar kowa kuma zabinta ta fada, kowa yayi na shi ba tare da an zage ta ba
Toyin Abraham, jarumar masana'antar shirya fina-finai ta Nollywood, ta ce goyon bayan ta ga Bola Tinubu, dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar APC, ba don kudi ba ne.
A watan Janairun 2023, jarumar fim din ta bayyana cewa zata iya zabar Tinubu saboda ta na ''son shi''.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewarta:
''Ina son Asiwaju kuma wannan ra'ayi na ne. Ina son shi. Kuma zan zabe shi don ina son shi. Duk da ban yanke shawara ba, ina fada muku dai kawai. Da kuma saboda abin da ya yi ga masana'antar mu."
Zabin dan takara da Toyin tayi ya jawo mata tarin zagi da yabo a kafafen sada zumunta.
A wani hirar kai tsaye ta manhajar Instagram tare da Kemi Afolabi, Toyin ta mayar da martani ga yan Najeriya da ke zaginta saboda ta goyi bayan Tinubu.
Ta ce wanda su ke zagin ta suna bata lokacin su saboda ''ban karbi ko kobo'' daga dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar APC ba.
Toyin ta ce ita ma yar kasa ce kuma bai kamata a zage ta saboda ta bayyana ra'ayin ta.
Ta cigaba da cewa:
''Duk wanda ya tsine min ko ya ke min fata, ba zai shafe ni ba saboda ban karbi kudi ba. Wanda suka karbi kudi kadai tsinuwar zata kama.
''Ni, Oluwatoyin, ban karbi kudi ba kuma ba wani na ke tallatawa ba amma muna tattaunawa ne saboda wannan kasata ce, yar Najeriya ce ni kuma a nan na haifi da na.
''Ba wanda zai iya biyana. Ina samun kudi na, ina siyar da fina-finai a manyan gidajen kallo, ina siyarwa a shafuka daban daban, ina samun kudi kuma ya ishe ni. Kawai za zabi dan takarar ka amma kada ka zage ni.''
Yan Najeriya za su fita kada kuri'a ranar 25 ga Fabrairu don zabar sabon shugaban kasa. Jimullar yan takara 18 ne za su fafata a zaben shugaban kasar.
Amma 4 daga ciki sun fi yiwuwar lashe zaben.
Sun hada da Tinubu, Peter Obi na jam'iyyar LP, Atiku Abubakar na PDP, da Rabiu Kwankwaso na NNPP.
Fitattun Fastoci 5 Da Ke Goyon Bayan Takarar Shugabancin Kasa Na Peter Obi
A wani rahoton kun ji cewa wasu fitattun fastoci a Najeriya sun fito karara sun nuna goyon bayansu ga takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi.
Wata sabuwa: Hadimar Aisha Buhari ta tafi kotu, ta ce matar Buhari ta ci zarafinta, a bata diyyar N100m
Daga cikinsu akwai Fasto Chris Oyakhilome wanda ya ce an masa wahayi cewa Obi ne mafi alheri ga Najeriya.
Asali: Legit.ng