'Yan Kasuwa Sun Yi Watsi da Umarnin CBN, Suna Ci Gaba da Karbar Tsoffin Kudi a Wurin Taron Tinubu

'Yan Kasuwa Sun Yi Watsi da Umarnin CBN, Suna Ci Gaba da Karbar Tsoffin Kudi a Wurin Taron Tinubu

  • Yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana game da halin da ake ciki na karancin Naira, ‘yan kasuwa sun ci gaba da karbar tsoffin kudi
  • A wurin taron gangamin kamfen Tinubu, an ga masu siyar da kayayaki na ciniki da tsoffin kudaden da suke kan ganiyar zama haramtattu a kasar
  • Wannan ne kamfen Tinubu na karshe gabanin babban zaben 2023 da za a yi a ranar Asabar 25 ga watan Faburairu

Jihar Legas - ‘Yan kasuwa na ci gaba da karbar tsoffin Naira yayin da Tinubu ke yin gangamin kamfen dinsa a birnin Legas.

Wannan ci gaba da karbar tsoffin kudi dai ya yi daidai da umarnin kotun koli na tsawaita ci gaba da karbar tsoffin kudin a Najeriya.

Idan baku manta ba, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sauya fasalin kudin Najeriya; N200, N500 da N1000 tare da sanya wa’adin daina amfani da tsoffin.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Ya Sabawa Kotun koli Wajen Dawo da Tsofaffin N200 Daga Hannun CBN

Ana ci gaba da karbar kudi a wurin taron gangamin APC
'Yan Kasuwa Sun Yi Watsi da Umarnin CBN, Suna Ci Gaba da Karbar Tsoffin Kudi a Wurin Taron Tinubu | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

‘Yan kasuwa a Legas na ci gaba da karbar tsoffin kudi

Wasu ‘yan kasuwa da suka zanta da jaridar The Nation a lokacin gangamin kamfen na Tinubu, sun ce karbar kudin ne hanya mafi sauki na taimakawa wadanda ke da tsoffin kudin a hannu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sun kuma shaida cewa, basu da wani zabin da ya wuce su ci gaba da karbar tsoffin kudin tunda har yanzu sabbi basu wadata a hannun jama’a ba.

Jaridar ta kuma lura cewa, siye da siyarwa ya yi sanyi a wurin taron duk da kuwa ana karbar tsoffin kudin da ke kan ganiyar daina amfani nan ba da jimawa ba.

Magoya bayan APC da suka ji dadin wannan lamari sun ci gaba da siyan kayan ‘yan kasuwan da suka zagaye filin wurin da ake gangamin a zagayen Legas.

Kara karanta wannan

CBN: Tinubu Ya Gabatar Da Babban Bukata 1 Bayan An Yi Zanga-Zanga Kan Karancin Naira a Fadin Najeriya

Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin mahukutan Najeriya game da sauyin kudi da kuma wa’adin daina amfani dasu.

Akwai kudi a kasa, bankuna sun ki zuwa dauka, inji CBN

A wani labarin, kun ji yadda Babban Bankin Najeriya (CBN) yace akwai tsabar kudi a kasa, kawai dai bankuna sun ki zuwa dauka ne.

Bankin ya bayyana cewa, akwai adadin kudade da yake ba kowane banki, amma ga kudi a kasa, ba a dauka ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.