Yan Sanda Sun Cafke Ɓata Gari Ɗauke Da Takardun Ƙuɗi Na Bogi

Yan Sanda Sun Cafke Ɓata Gari Ɗauke Da Takardun Ƙuɗi Na Bogi

  • Ƴan sandan a jihar Kebbi sun yi wani babban kamu inda suka samu nasarar cafke wasu ɓata gari a jihar
  • Hukumar ƴan sandan jihar ta cafke wasu miyagun ɓata gari ɗauke da takardun sababbin kuɗin naira na bogi
  • Tuni hukumar ta kammala binciken ta inda zata gaggauta tura su zuwa kotu domin fuskantar hukuncin da ya dace da su

Kebbi - Hukumar ƴan sandan jihar Kebbi tayi wani babban kamu inda ta samu nasarar cafke wasu ɓata gari ɗauke da takardun sababbin kuɗi na bogi.

Hukumar ƴan sandan ta samu nasarar cafke mutanen guda uku ɗauke da tsaɓar takardun sababbin kuɗi har na naira miliyan goma sha bakwai (N17m). Rahoton Daily Trust

Sabbin kuɗi
Yan Sanda Sun Cafke Ɓata Gari Ɗauke Da Takardun Ƙuɗi Na Bogi
Asali: Getty Images

Ƴan sandan sun samu nasarar cafke ɓata garin ne a yankin Warrah cikin jihar Kebbi dake a yankin Arewa maso Yamma na Najeriya.

Kara karanta wannan

"Wannan Cin Mutunci Ne" Gwamna Wike Ya Ƙara Fusata, Ya Yi Wa Atiku Tatas Ana Saura Kwana 5 Zabe

Kwamishinan ƴan sandan jihar, Ahmed Magaji Kontagora, shine ya tabbatar da cafke ɓata garin. Rahoton jaridar Guardian

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kwamishinan ƴan sandan na jihar ya bayyyana cewa an cafke waɗanda ake zargin ne a tashar mota ta Warrah a jihar Kebbi.

Ya kuma bayyana cewa ƴan sanda sun samu nasarar cafke waɗanda ake zargin ne tare da taimakon mambobin ƙungiyar direbobin motoci ta ƙasa (NURTW) dake a tashar mota ta Warrah.

Ya bayyana sunan waɗanda ake zargin da Faruku Zubairu, Ibrahim Musa da Salisu Mohammed, waɗanda suka fito daga ƙauyukan Gungun Tawaye da Chupamini a ƙaramar hukumar Ngaski ta jihar.

Kwamishinan ya kuma ƙara da cewa tuni suka kammala binciken su inda za a tura waɗanda ake zargin zuwa kotu domin fuskantar hukunci kan laifukan da suka aikata.

Yadda Na Dakatar Da Kuɗirin Tazarcen Obasanjo -Atiku Abubakar

Kara karanta wannan

Talaka Na Shan Wuya, Duk Da Ina Gwamna Sababbin Kuɗin Sun Yi Min Wuyar Samu -Gwamna Ya Koka

A wani labarin na daban kuma, ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP ya bayyana yadda ya kawo cikas ga kuɗirin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo na yin tazarce akan mulki.

Atiku Abubakar ya yiwa Olusegun Obasanjo mataimakin shugaban ƙasa tun daga shekarar 1999 har zuwa 2007.

Sai dai dangantaka tayi tsami a tsakanin shugabannin biyu gab da kammaluwar wa'adin su akan madafun iko na Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng