Kai Tsaye: Yadda PDP Ke Gudanar Kamfen Karshe Yau A jihar Adamawa

Kai Tsaye: Yadda PDP Ke Gudanar Kamfen Karshe Yau A jihar Adamawa

Jirgin yakin neman zaben takarar kujerar shugaban kasan Najeriya a zaben 2023 na jam'iyyar PDP ya zo karshe inda dan takarar jam'iyyar ya dira jiharsa ta Adamawa.

Taron na gudana kai tsaye yanzu a farfajiyar Ribadu dake birnin Yola, jihar Adamawa

Ban taba ganin irin wannan taro ba: Jawabin Atiku Abubakar

Atiku yace:

Al'ummar Adamawa, yau ne ranar karshen kamfenmu a fadin kasar nan.
Ina godewa yan Najeriya da suka nuna min soyayya da jam'iyyarmu. Ba Zamu taba kunyata ku ba idan kuka zabemu.
Mun yi alkawarin zamu cika alkawarin hada kan Najeriya, samar da zaman lafiya a kasar, zamu inganta tattalin arziki, zamu inganta ilimi kuma zamu mayar da mulki hannun jihohi da kananan hukumomi.
Wadannan sune abubuwa biyar da PDP tayi alkawari.
Al'ummar Adamawa kuwa ni ba bakonku bane. Kada ku bari wani ya yaudare ku. Ina kira gareku ku tabbatar da cewa kun zabi dukkan yan takara na PDP.
Yan Adamawa, kada ku ba yan Najeriya kunya

Jawabin Shugaban Uwar Jam'iyyar PDP, Iyorchia Ayu

Shugaban uwar jam'iyyar PDP, Iyorchia Ayu, ya bayyana cewa duk inda suka je yayin kamfen nan sun amince Atiku ya zama shugaban kasan Najeriya.

Ayu ya bayyana cewa gwamnatin jam'iyyar APC ta jefa Najeriya cikin kangin wahala kuma gashi yanzu suna rigima tsakaninsu.

A cewarsa, gwamnonin APC sun boye kudade shiyasa suke fito-na-fito da shugaba Muhammadu Buhari.

"Wannan shine karo na biyu da zamu kwato Najeriya daga kangin matsala. Na farko shine a 1998 lokacin da muka kafa PDP. Yanzu kuma samu sake ceto ta."

Jam'iyyu siyasa 5 sun sanar da marawa Atiku baya

Wasu jam'iyyun siyasa biyar sun sanar da watsi da yan takararsu na shugaban kasa kuma suna marawa Atiku Abubakar baya.

Jam'iyyun sun hada da Allied Peoples Movement APM, Action Alliance AA, National Rescue Movement NRM, African Democratic Congress ADC da APP.

Shugaban jam'iyyar APM, Yusuf Mamman Dan Talle, yayi jawabi madadi wadannan jam'iyyu a filin kamfen dake gudana a Adamawa.

Yusuf Mamman Dan Talle a jawabinsa ya bayyana cewa:

"Ina nan zan gabatar da jawabi a madadin jam'iyyun siyasa biyar da suka yanke shawarar mara goyon baya ga Atiku Abubakar.
Lokaci yayi da zamu hada kai, mu daura kasar nan kan turbar shiriya. Lokaci yayi na kawo karshen wahala a kasar nan.
Lokaci ya yi na kawo karshen mayar da wasu saniyar ware a kasar nan.
Domin cigaba da kasar nan, mu shugabannin jam'iyyu biyar bayan shawara da masu ruwa da tsaki, mun yanke shawara zaben Atiku Abubakar da Ifeanyi Okowa ranar zaben shugaban kasa.
Mun yi imanin cewa Atiku/Okowa ne masu kwarewa a zaben nan.
Najeriya na bukata mai bauta, gwamnati mai saurarar kukan mutane, gwamnati da zata mayar da mayar hankali kan tsaro da lafiya jama'a kamar da kundin tsarin mulki ya tanada.
Wadannan jam'iyyun biyar zasu rusa tawagarsu don kamfen Atiku/Okowa.
Muna da tabbacin cewa Atiku/Okowa zasu ci zabe."

Kada muyi kuskure, Atiku Abubakar ne zai iya kai Najeriya ga gaci.: Tambuwal

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana cewa kada yan Najeriya su sake tafka kuskuren baya wajen zaben jam'iyyar APC.

Tambuwal wanda shine Diraktan Kamfen Atiku, ya ce kukan kurciya jawabi ne, kuma sai mai hankali ke ganewa.

Ya yi kira ga al'ummar Adamawa cewa ko wani tsuntsu kukan gidansa yake, saboda haka kada su baiwa Atiku kunya.

Ya ce su fito su zabi Atiku da PDP daga sama har kasa.

Yace:

"Mun fara kamfe ranar 10 ga Oktoba 2022 a Uyo jihar Akwa Ibom, tun daga ranar mun shiga kowani lungu da sakon kasar nan na mu mai girma kuam dan takararmu na da magoya baya sosai.
Muna da tabbacin cewa zamu samu nasara.
Mu ba yan tsautsauran masu ra'ayin addini bane kuma mu ba yan kabila bane. Dan takararmu ya gabatarwa yan Najeriya manufofi biyar da zamu yi kuma Atiku da Okowa na shirin aiwatar da su tun ranar hawa mulki.
Sauran yan takaran basu kai Atiku kwarewa ba ko kadan. Kada muyi kuskure, Atiku Abubakar ne zai iya kai Najeriya ga gaci.
Yanzu ya bayyana karara cewa Atiku/Okowa ke shirye da jagorantar kasar nan cikin hadin kai.
Kada mu sake kuskuren zaben APC, mun ga abinda muke ciki.

Babu wanda ya fahimci Najeriya kamar Atiku: Tsohon Shugaban Majalisa, Bukola Saraki

Tsohon Gwamnan jihar Kwara kuma Tsohon Shugaban majalisar dattawan tarayya, Abubakar Bukola Saraki, ya bayyana cewa kada yan Najeriya suyi kuskure su zabi APC.

Saraki yace a wannan taro na karshe, yan Najeriya su zabi wanda ba dan koyo bane, masani ake bukata.

A cewarsa:

"Babu wanda ya fahimci Najeriya kamar Wazirin Adamawa
Babu wanda ya fahimci kasuwanci kamar Wazirin Adamawa
Wannan ba lokacin gwaji bane, lokacin kwararre ne
Ku zabi mutumin da ya fitar da mu daga wannan kangin da muke ciki."

Saraki
Kai Tsaye: Yadda PDP Ke Gudanar Kamfen Karshe Yau A jihar Adamawa
Asali: Depositphotos

Online view pixel