Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Zai Yiwa Yan Najeriya Jawabi a Ranar Alhamis
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yiwa 'yan Najeriya kan halin da ake ciki a kasar nan da kuma mafita
- Ana kyautata zaton jawabin zai mai da hankali ne ga yadda karancin sabbin Naira ke shafar rayuwar 'yan Najeriya
- 'Yan Najeriya na ci gaba da fuskantar kalubale tun bayan kaddamar da sabbin kudi a kasar a shekarar da ta gabata
FCT, Abuja - A ranar Alhamis da misalin karfe 7 na sanyin safiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yiwa 'yan kasa jawabi, The Nation ta ruwaito.
Wannan na fitowa ne daga bakin mai ba shugaban kasa shawari kan harkokin yada labarai, Femi Adesina a cikin wata sanarwar da ya fitar.
Adesina ya bayyana cewa, za a yada jawabin shugaban kasan a gidajen talabiji, rediyo da sauran kafafen yada labarai na kasar.
Ya zuwa yanzu dai ba san dalilin da yasa shugaban kasan zai yiwa 'yan Najeriya jawabi ba a daidai lokacin da 'yan kasar ke cikin matsi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jawabin na shugaban kasa dai na zuwa ne daidai lokacin da 'yan Najeriya ke ci gaba da kuka kan yadda karancin takardun Naira ya shafi rayuwarsa ta yau da kullum.
'Yan Najeriya na fama da karancin Naira, suna ta zanga-zanga
Gabanin bayyana jawabin Buhari, kasar nan na fama da rikici tun bayan da kowa ya nemi sabbin Naira ya rasa.
An yi zanga-zanga a bangarori daban-daban na Najeriya don nuna adawa da shirin gwamnatin tarayya kan ka'idar sabbin kudi.
An kone bankuna, an fatattaki ma'aikatan banki, musamman a jihohin Kudancin kasar duk dai don jawo hankalin gwamnati ya karkata ga hakin da 'yan kasar ke ciki.
Akwai kudi a kasa, CBN ya musanta karancin kudi
A bangare guda, CBN ya ce ya buga wadatattun kudin da za a iya ba kowa a Najeriya a bankunan kasuwanci, amma ya bayyana inda matsalar take.
A cewar CBN, bankunan kasuwanci sun ki zuwa daukar sabbin kudin da aka buga, sun bar kwastomominsu na bin layin wahalar cire kudi a ATM da kan kanta.
Ya zuwa yanzu, 'yan kasar na ci gaba da nuna koke, sun gaza fahimtar gwamnati, gwamnati ta gaza fahimtarsu.
Asali: Legit.ng