Yanzu Yanzu: Ana Zanga-Zanga a Jihohin Ondo, Kwara, Delta Kan Karancin Sabbin Naira da Kin Karbar Tsoffin Kudi
- Har yanzu yan Najeriya na fama da wahala sakamakon rashin wadatattun sabbin kudi da kuma kin karbar tsoffin kudi
- Mutane da dama musamman matasa sun fito don yin zanga-zanga a jihohin Ondo, Kwara da Delta
- Fusatattun yan Najeriyan suna neman gwamnatin tarayya da ta kawo masu dauki a yayin da suke cikin wani yanayi na wayyo Allah
Wasu mazauna garin Ondo da ke karamar hukumar Ondo ta yamma a jihar Ondo sun fito tituna a ranar Laraba, 15 ga watan Fabrairu don gudanar da zanga-zanga a kan karancin sabbin Naira da kuma kin karban tsoffin kudi da bankuna ke yi.
An gano mazauna yankin wadanda yawancinsu matasa ne suna tattaki a tati don yin zanga-zangar lumana, jaridar Leadership ta rahoto.
Zanga-zangar wanda ya gudana a shahararren shataletalen nan na tashar motar Akure ya yi sanadiyar sanya shinge a kan titi wanda ya haifar da cunkoson ababen hawa a titin.
An cinnawa tayoyi wuta a hanyar yayin da jami'an rundunar yan sanda ke shawagi a wajen don sanya ido kan yadda zanga-zangar ke gudana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakazalika, a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, an toshe hanyoyi don yin zanga-zanga a kan karancin sabbin kudin da kuma kin karbar tsoffin kudi da yan kasuwa ke yi a yankunan Oloje da Oko-Olowo na jihar.
Matasa sun yi barna yayin zanga-zanga a jihar Delta
Lamarin ya sha banban a jihar Delta domin ba cikin lumana ake zanga-zangar ba yayin da aka rahoto cewa matasa sun cinna wuta a wani ATM don zanga-zanga kan mawuyacin halin da suka shiga sakamakon rashin sabbin kudi a Warri.
Sahara Reporters ta rahoto cewa fusatattun matasan na zanga-zanga a yankin Udu inda suka tarwatsa motoci da lalata kayayyaki a yankin.
CBN ya saki hanyoyin kai karar masu POS da ke siyar da sabbin kudi
A wani labarin, mun ji cewa babban bankin Najeriya ya saki hanyoyin da yan Najeriya za su kai karar masu POS da ke siyar da sabbin kudi yayin da ake fama da karancinsu a kasar.
Haka kuma CBN ya saki lambobin waya da za a iya kira don kwarmata masa kan masu yin chaji da ya yawa yayin cire kudi a POS.
Asali: Legit.ng