Ta Hadu: Bidiyon Yadda Wata Kyakkyawar Budurwa Mai Kafa Daya Ta Tika Rawa Cike Da Kwarewa Ya Ja Hankali
- Wata kyakkyawar budurwa yar Najeriya mai kafa daya ta burge zukata soshiyal midiya da bidiyon rawanta
- A wata wallafa da ta yi a TikTok, matashiyar ta takarar rasa cikin kwarewa kuma jama’a sun yaba kyawunta
- Da suke martani ga bidiyon, wasu jama’a sun nuna soyayyarsu gareta sannan su yi mata addu’ar ci gaba da dawwama a farin ciki
Wata matashiyar budurwa yar Najeriya, Cindy Chilaka, ta shahara a soshiyal midiya bayan ta wallafa bidiyon rawanta a TikTok.
A bidiyon mai kayatar da zuciya, an gano matashiyar tana rawa yayin da masu amfani da soshiyal midiya ke yaba kyawunta.

Asali: TikTok
Sanye da jan tufafi da gajeren wando, kyakkyawar budurwar ta girgiza jikinta daidai da kidan sautin da ke tashi a bidiyon.
Jama’a da suka ci karo da bidiyon a TikTok sun yi jinjina a gareta tare da yaba karfin gwiwarta.

Kara karanta wannan
Shugaba Buhari Ya Roki Gwamnatin Dubai Ta Cirewa yan Najeriya Takunkumin Hana Shiga
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jama’a sun yi martani
@reshapeupyourshape ta ce:
“A zahirin Gaskiya, Allah madaukakin sarki yana da mu’ujiza. Tsayuwa a kan kafa daya kawai tare da yin rawa haka alhalin mu masu kafa biyu ba Za mu iya haka ba! Ma shaa Allah!”
@mimzytik ta ce:
“Na so karfin gwiwar ki yar’uwa. Wannan shine abun da kawai zai sa ki farin ciki kwasar nishadi ba tare da duba nakasarki ba..waw.”
@frankad18 ya rubuta:
“Ke ta daban ce. Na kasa iya tsayar da hawayena da na ga cewa kina matukar farin ciki. Ina taya ki murna yar’uwa.”
@ladyklassik ta ce:
“Kina da kyau sosai, Ina ganin ta taba haduwa da ke, mun shiga mota daya daga Ph zuwa mbaise.”
Kalli bidiyon a kasa:
Babu ni babu yiwa namiji tayin soyayya, budurwa ta bayyana yadda wani da ta so ya bada mata kasa a ido

Kara karanta wannan
Babu Kunya: Budurwa Ta Ziyarci Mahaifinta Mai Tabin Hankali a Ranar Bazdai Dinsa, Ta Yi Rawa Tare Da Shi a Bidiyo
A wani labarin, wata kyakkyawar budurwa ta bayyana yadda abubuwa suka kaya tsakaninta da wani matashi da ta hadu da shi a soshiyal midiya.
Matashiyar dai ta bibiyi shafin saurayin wanda ta ga ya yi mata sannan ta yi masa magana amma ya dungi amsa mata a dakile.
Bata yi kasa a gwiwa ba inda ta tambaye shi ko bai da budurwa amma ya ce mata yana da ita.
Asali: Legit.ng