Yanzu Aka Fara: DSS Tace Bata Gama Tuhumar Fani-Kayode ba
- Hukumar Jami’an Tsaron Farin Kaya ta ce har yanzu ba ta gama tuhumar tsohon ministan Sufurin jirage, Femi Fani-Kayode ba
- Tsohon ministan, wanda shi ne Daraktan kungiyar kamfen din Bola Tinubu ya yi barin zance na cewa, Atiku da wasu manyan soji su na shirye-shiryen juyin mulki
- DSS ta bayyana yadda ta bada belinsa ba tare da ko ficika ba, yayin da zata cigaba da tsitsiyeshi har zuwa kammala bincike, daga bisani ta shawarci 'yan siyasa da su guji furta kalaman tada tarzoma a fadin kasa
FCT, Abuja - Hukumar jami’an tsaron Farin Kaya a ranar Laraba ta ce bata gama tuhumar tsohon ministan Sufurin jirage wanda shi ne Daraktan kungiyar kamfen din 'dan takarar shugaban kasar jam'iyyar APC, Femi Fani-Kayode ba.
DSS ta gayyaci Fani-Kayode ranar Litinin kan wasu jerin wallafe-wallafe da ya yi a Twitter a karshen mako, wanda ya ke ikirarin wasu manyan soji sun gana da 'dan takarar shugaban kasar jam'iyyar PDP, Atiku Abubukar don shirya juyin mulki.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Duk da dai, Fani-Kayode, bayan tuhumarsa jiya, ya amince da kuskuren da ya yi na gaza warware zare da abawa ga hukumomin da suka dace kafin furta maganar da ta jawo cecekuce, inda ya kara da cewa, da ya sani da ba haka ya yi ba.
Sai dai, bayan titsishi na awanni biyar, DSS ta ce har yanzu ba a rufe shafin tuhumar tasa ba, jaridar Punch ta rahoto.
Haka zalika, hukumar ta gargadi jam'iyyun siyasa da su iya da bakinsu yayin lokacin zabe.
Vanguard ta ruwaito cewa, a wata takarda da DSS kakakin DSS, Peter Afunanya ya saki ta nuna cewa:
"Hukumar Tsaron Farin Kaya ta na son sanar da al'umma cewa ta gayyaci Cif Femi Fani-Kayode zuwa da hedkwatarta na Abuja, ranar 13 ga watan Fabrairu, 2023. Gayyatar sakamakon wani bincike ne game da zargin da ya ke wanda barazana ne ga zaman lafiyar kasa.
"Cif Femi Fani-Kayode ya fuskanci jerin tambayoyi game da furucinsa. Daga bisani, hukumar ta bada belinsa gami da umartarsa da ya dawo ranar Laraba, 15 ga watan Fabrairu, 2023 har zuwa kammala bincike. Yayin da za a cigaba da binciken.
"Sai dai, ana shawartar jam'iyyun siyasa da masu kula da shafikan yanar gizo da su san mai ya kamata su furta da sakon da ya kamata su isar kafin ko bayan gangamin zabe me karatowa. Wannan duk don guje wa jawo rikici da tada tarzoma wanda barazana ne ga zaman lafiyar al'umma."
Gwamnan Zamfara ya umarci duk NGOs su bar jihar
A wani labari na daban, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya umarci dukkan NGOs da su bar fadin jihar.
Gwamnan yace yana zarginsu da assasa rashin zaman lafiya a fadin jihar.
Asali: Legit.ng