Mun Shirya Buga Isassun Sabbin Kudi: Kamfanin Buga Kudin Najeriya, NSPM
- Kamfanin Minting ya yi watsi da labarin cewa ba su da kayan aikin buga sabbin kudin Najeriya
- Najeriya na fama da karancin tsabar kudi cikin al'umma kuma ana cikin mawuyacin hali
- Majalisar magabata ta bukaci CBN ya buga sabbin kudi ko kuma ya fito da tsaffin kudin mutane
Abuja - Kamfanin buga kudin Najeriya (NSPM) ta bayyana cewa ta gama shirye-shiryen cigaba da buga sabbin kudin Najeriya da aka sauyawa fasali.
Wannan ya biyo bayan labarin da ke yawo cewa babban bankin Najeriya CBN ya bayyana rashin isassun kayan aikin buga kudaden a masana'antar NSPM.
Shugaban kamfanin, Ahmed Halilu, ya yi watsi da labarin inda yace suna da isassun kayan aikin buga sabbin kudi, rahoton TheCable.
Hakazalika ya yi watsi da cewa kamfanin De-La-Rue na kasar Birtaniya ne ke bugawa Najeriya kudi inda yace ko takardu kamfanin bai sayarwa Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A jawabin kamfanin ya fitar, ya ce:
"Kamfanin buga takardun kudin Najeriya watau Nigerian Security Printing and Minting (NSPM) ya samu labarin da ake nasabtawa gwamnan bankin CBN kan cewa kamfanin NSPM ba zai iya cigaba da buga sabbin kudi ba saboda rashin kayan aiki."
"Bayan CBN ya yi watsi da wannan labari, muna son mu kara da cewa kamfanin De-la-Rue na Birtaniya bai bugawa Najeriya kudi hakazalika bai sayarwa kasar nan takardu."
"Muna son jaddadawa yan Najeriya cewa NSPM ta shirya komai don cigaba da buga takardun kudi bisa tsarin CBN na 2023."
Majalisar Magabatar Najeriya sun baiwa gwamnan CBN zabi guda
Majalisar tsaffin shugabannin Najeriya da masu masu fada a aji sun bayyanawa gwamnan babban bakin Najeriya CBN ra'ayinta game da lamarin sauya fasalin kudi.
Majalisar ta ce tana nuna goyon bayanta ne da sharadin bankin ya dau matakan gaggawa don tabbatar yan Najeriya sun samu isassun tsabar kudi a fadin kasa.
Sun bukaci gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya samar da isassun sabbin takardun Naira ko kuma ya fitar da tsaffi mutane suyi amfani.
Emefiele dai har yanzu bai fadi matsayar da ake ciki ba amma har yanzu yan Najeriya na fama da rashin tsabar kudi.
Legit ta ji ta bakin wani mazaunin birnin tarayya a Abuja wanda ya bayyana yadda ya nemi tsabar kudi sama da kasa amma bai samu ba.
Malam Ishaq ya bayyana cewa kusan dukkan masu POS dake unguwarsa ta Lokogoma babu da tsabar kudi.
Asali: Legit.ng