Zagaye Na Biyu, Emmanuel Bwacha Ya Lashe Zaben Fidda Gwanin APC a Taraba

Zagaye Na Biyu, Emmanuel Bwacha Ya Lashe Zaben Fidda Gwanin APC a Taraba

  • Bayan kai ruwa rana kotunan Najeriya uku, Emmanuel Bwacha ya sake lashe zaben fidda gwani
  • Jam'iyya APC ta shiga rikita-rikita game da wanda zai yi mata takara a zaben gwamnan bana
  • Abokan hamayyar Sanata Bwacha sun ce ba tare da su akayi wannan zaben ba, tumun dare ne

Sanata mai wakiltar mazabar Taraba ta kudu, Emmaneul Bwacha, ya lashe zaben fidda gwanin dan takarar gwamnan jihar Taraba na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Wannan shi ne zagaye na biyu na zaben kuma Tukur Buratai, tsohon shugaban hafsun Soji ya jagoranci kwamitin zaben.

Bwacha
Zagaye Na Biyu, Emmanuel Bwacha Ya Lashe Zaben Fidda Gwanin APC a Taraba Hoto: Emmanuel Bwacha
Asali: Twitter

Kotun koli a ranar 1 ga Febrairu toa soke zaben fidda gwanin da akayi a 2022 inda Bwacha yaci zaben farko.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Ku Da Kanku Kun Amince Akwai Kura-Kurai A Zaben, Atiku Ya Fada Wa Bangaren Tinubu

Kwamitin Alkalan karkashin Kudirat Kekere-Ekun ta tabbatar da cewa lallai da farko ba'a gudanar da zaben kirki ba kuma tayi umurnin a sake sabon zabe cikin kwanaki 14.

Ranar Juma'a 10 ga wata jam'iyyar ta zaba domin gudanar da sabon zaben.

Bayan kammala zaben, Bwacha ya samu kuri'u 778 yayinda abokin hamayyarsa, Yusuf Yusuf, ya samu kuri'u 5 kacal, rahoton TheCable.

Buratai ya ce mutum 796 aka tantance cikin deleget 840 da aka gayyata.

Bwacha ya bayyana farin cikinsa bisa wannan nasara kuma yace wannan ya sake tabbatar da cewa mutane na tare da shi.

APC ta zabi ranar sabon zaben fiddan gwanin dan takarar gwamna

A baya kun ji cewa Uwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta sanar da ranar gudanar da sabon zaben fidda gwanin dan takarar gwamnan jihar Taraba a zaben 2023 da zai gudana.

APC ta zabi ranar Juma'a, 10 ga watan Febrairu, 2023 kamar yadda wasikar ya nuna.

Kara karanta wannan

Sakamakon Zaben 2023: Atiku Ya Bayyana Matakin Karshe Da Zai Dauka Idan Bai Yi Nasara A Kotu Ba

Wannan ya biyi bayan shari'ar kotun kolin Najeriya na ranar Lahadi wanda ya yi watsi da Sanata Emmanuel Bwacha a matsayin dan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar APC.

A wasika mai dauke da ranar wata, 2 ga Febrairu, 2023, Sakataren tsare-tsare na jam'iyyar, Sulaiman Muhammad Argungun, ya bayyana shugaban APC na jihar cewa za'a yi zaben fidda gwanin ne a filin kwallon Jolly Nyame dake Jalingo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel