Yan Ta'adda Sun Kashe Mutum 5, Sun Kona Fadar Basarake Da Wasu Gidaje Fiye Da 50 A Benue
- Wasu mahara da ba a san ko su wanene ba sun afka wa mutane a garin Nagi da ke karamar hukumar Gwer a jihar Benue
- Maharan sun halaka mutane biyar, mata biyu da maza uku sannan sun kona gidaje fiye da 50 ciki har da fadar basaraken garin na Gwer
- Hadimin gwamnan jihar Benue a yankin ya tabbatar da afkuwar harin amma ya ce dakarun sojoji sun kawo wa al'umma dauki sun kuma fatattaki maharan
Jihar Benue - An kashe a kalla mutane biyu bayan da wasu mahara suka kai hari garin Nagi da ke karamar hukumar Gwer ta Yamma na jihar Benue.
An kuma raunata wasu mazauna garin guda bakwai yayin harin da ya faru misalin karfe biyar na yammacin ranar Alhamis, Daily Trust ta rahoto.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mazauna kauyen sun ce maharan ta farko sun bude wuta ne ga mutane a garin Naka, hedkwatar karamar hukumar Gwer amma jami'an tsaro suka fatattake su.
Sun ce yan bindigan sun tsere amma daga bisani suka kai hari garin Nagi inda suka kashe mutane biyar - mata biyu da maza uku, yayin da suka kone gidaje fite da 50 ciki har da fadar sarkin gargajiya na garin.
Hadimin gwamnan Benue ya tabbatar da harin
Mashawarci na musamman ga gwamnan jihar Benue, Laftanat Kwanal Paul Hemba, a ranar Juma'a ya tabbatar da afkuwar harin yayin da ya ke magana da manema labarai a Makurdi, ya yi ikirarin cewa:
"Su maharan, sun taho kamar yadda suka saba, hari ne kawai na babu gaira babu dalili.
"Amma da barnar da aka yi ya fi hakan idan ba domin daukin gaggawa da jami'an sojoji suka kawo ba suka fatattake su.
"Mutane biyar sun mutu. An tsaurara matakan tsaro kuma an karo sojoji kuma sunyi nasarar daidaita al'amura a yankin. Yanzu komai ya koma daidai."
Rayuka a kalla 16 sun salwanta a wani harin da aka kai jihar Benue
A wani rahoton kun ji cewa kimanin masu sayar da katako na timba 16 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon harin da yan ta'adda suka kai musu a Mbagwen suna harbin kan mai uwa da wani
Caleb Abba, shugaban karamar hukumar Guma ya tabbatar da afkuwar harin da ya ce an kai misalin karfe 7 na yammacin ranar Litinin.
Asali: Legit.ng